Bapalasdine ya kera samfurin Marsandi kirar 1927
Wani Bapalasdine, mai gyaran mota a zirin Gaza, mai suna Munir Shindi, ya ga wata mota kirar Marsandi ta shekarar 1927, mai kofa, al’amarin da ya ja hankalinsa, ya dukufa said a ya kera irinta.Bapalasdine ya yi amfani da kangarwar tsofaffin motoci wajen kera sassan jikin motar, sannan ya sanya aka shigo masa da mkullai […]
Wani Bapalasdine, mai gyaran mota a zirin Gaza, mai suna Munir Shindi, ya ga wata mota kirar Marsandi ta shekarar 1927, mai kofa, al’amarin da ya ja hankalinsa, ya dukufa said a ya kera irinta.
Bapalasdine ya yi amfani da kangarwar tsofaffin motoci wajen kera sassan jikin motar, sannan ya sanya aka shigo masa da mkullai da marikan kofofi daga kasr Amurka.. Shindi matashi ne mai shekara 36, ya shafe shekara biyu wajen kera motarsa.
“Ina son tabbatar wa kaina cewa zan iya, kuma ba za a ce abu bu ne da bai yiwuwa ba,” inji shi. Yace har yanzu yana jiran hukuma ta ba shi izini da lasisin da za su ba shi damkar tukawa. Asalin kirar motar dai zanen Ferdinand Ponsche ne, an kuma yi mata zayyana da launin barewa, al’amarin day a sanya Marsandi ta sha gaban ababen hawa a shekarun 1920 zuwa 1930.
A bayanin da ke kunshe a shafin sadarwar mota, an bayyana cewa nau’ukan Marsandi 300 da aka yi musu lakabi da Gazelle aka kera, kuma daya daga cikin wadancan nau’uka da aka sake ytin irin fasalinta, an sayar da ita Dala miliyan bakwai da dubu 400 cikin shekarar 2004.
Palasdinawan Gaza da ke karkashin mulkin kungiyar Musulunci ta Hamas sun saba shigo da motoci daga sassan duniya ta Isra’ila. Akwai kimanin motoci dubu 70 da ke da rajista a yankin. Al’ummar yankin dai ba su wuce miliyan guda da dubu 950.