Baqin haure ne suka lalata Jam’iyyar PDP – Baffa Disina
Wasu dalilai ne suka sa ka fito takarar shugabancin Jam’iyyar PDP?Abin da ya sa na fito takarar shugabancin Jam’iyyar PDP a jiharmu ta Bauchi, shi ne mun fahimci cewa wasu baqin haure sun lalata mana jam’iyyar wadda muka dauki tsawon lokacin muna yi mata hidima tare da jaddada manufofinta a ciki da wajen Jihar Bauchi. […]
Wasu dalilai ne suka sa ka fito takarar shugabancin Jam’iyyar PDP?
Abin da ya sa na fito takarar shugabancin Jam’iyyar PDP a jiharmu ta Bauchi, shi ne mun fahimci cewa wasu baqin haure sun lalata mana jam’iyyar wadda muka dauki tsawon lokacin muna yi mata hidima tare da jaddada manufofinta a ciki da wajen Jihar Bauchi. Duk mutumin da yake tsoron Allah ya san cewa akwai kura-kurai da aka tafka a wannan jam’iyya ta PDP wasu da niyya aka yi su, wasu kuma sun faru ne saboda wasu dalilai. A baya mun sha ba da shawari game da yadda za a gyara tafiyar amma sai aka qi dauka. Daga bisani wadansu mutane ’yan tsirari da ba su san yadda aka yi aka gina jam’iyyar ba suka lalata PDP a Jihar Bauchi. Saboda haka muna cike da baqin ciki da rashin jin dadi game da yadda aka lalata mana PDP. Abin da ya haifar da haka shi ne shugabannin da suka gabata sun watsar da mutanen da suka yi wahala wajen kafa jam’iyyar ba sa kiran kowa domin tattauna abubuwan da suke wakana, su kadai suke gudanar da abubuwansu. Akwai dimbin mutane a Jihar Bauchi da ba su fita daga PDP ba, amma ba sa yi mata aiki, wasu kuma suna PDP amma suna aiki ga wata jam’iyya, haka jam’iyyar ta zo har zuwa lokacin da aka gudanar da zaben bara. Mutum uku ne kadai suka rasu daga cikin wadanda aka kafa PDP tare da su a jihar, wato marigayi Shettiman Katagum da Alhaji Inuwa Kwance-kura da marigayi Alhaji Maigari Yarima Papa sauran fitattun mutane da aka yi wahala da su wajen kafa PDP duk suna raye. To ganin yadda al’amura suke a PDP ya sa na fito wannan takara, kuma a qashin kaina babu wanda ya ce Baffa Disina fito takara domin ni ba yaron wani ba ne a siyasar Jihar Bauchi kuma na wuce in yi siyasar ubangida. Na wuce lokacin da wani mutum ko gungun mutane za su yi amfani da ni domin wata manufa ta siyasa, duk abin da ake nema a rayuwa Allah Ya ba ni gwargwado. Siyasar ubangida ce ta lalata PDP a Jihar Bauchi domin wanda za a sa ba ya da wani ra’ayi sai na ubangidansa. Amma kuma ya kamata a fahimci cewa ina da dimbin masoya a cikin manyan mutane a siyasar jihar. Ba ni da kudin da zan raba wa mutane domin ban saci kudin kowa ba, amma ina da abin da ya fi kudi idan aka ba ni dama to tabbas zan gyara abubuwan da suka lalace a PDP. Mutanen da suka yi fushi za mu ba su haquri su dawo a yi wa jam’iyya aiki. Ba na jin dadi in ga dan Jam’iyyar PDP yana munanan maganganu a kan jam’iyyar wadda muka dauki tsawon lokaci muna gina ta muna yi mata hidima kuma ba na jin dadi in ga dan PDP yana shan baqar wahala a rayuwa.
Idan wasu suka ce ka dakata daga wannan takara za ka amince?
Ina so ka fahimci cewa ban fito takara don in janye ba, zan ci gaba da neman wannan kujera saboda ina da manufofi masu kyau ga PDP, ba ina siyasa ba ne don neman tara abin duniya.
Me za ka ce game da kame-kamen da Hukumar EFCC ke yi wadanda mafi yawan ’yan PDP ne?
Abin da zan fada game da wannan tambaya shi ne babu wanda ya taba aike na da wani kaya domin in raba wa mutane a ce na cinye. Saboda haka a nawa ra’ayin kowa ya san cewa talakan Najeriya yana cikin uquba na talauci da rashin abin da zai ciyar da iyalansa. Amma tabbas ba na goyon bayan wadanda suka cinye kudin sayen makamai. Ina goyon bayan duk wanda ya ci kudin al’umma ba bisa qa’iba a tilasta masa ya dawo da su, kuma doka ta yi aiki a kansa ko daga wace jam’iyya ya fito.
Ka gamsu da manufofin Shugaban Qasa Buhari?
Na gamsu da wasu daga cikin manufofinsa, wadanda suka yi daidai da hankalina, rashin gaskiya ba ya da kyau. Jam’iyyar PDP ba ta yi wa kowa laifi ba a Najeriya, amma mutanen da aka ba su shugabancin jam’iyyar ba su riqe ta tsakani da Allah ba, daga bisani Allah Ya qwace mulkin daga wajenmu.
Duk Jihar Bauchi babu wani dan siyasa da zai ce ana rikici da Baffa Disina a kan abin duniya kullum abin da nake buqata shi ne a yi adalci ga kowa da kowa.
Kana ganin PDP za ta kafa gwamnati a Jihar Bauchi a shekarar 2019?
Abin da ya lalata siyasa a Najeriya shi ne kudi. idan ba ka da kudi babu wanda zai yi da kai, mafi yawan wadanda suke ba da kudin ba kudinsu ba ne kudin al’umma suka dauka. Sannan ina tabbatar maka da cewa Jam’iyyar PDP za ta sake kafa gwamnati a zaben shekara ta 2019, PDP tana nan lami lafiya amma shugabanninta ne suka lalata abubuwa. Jam’iyyar APC ba ta taba tsammanin za ta kafa gwamnati a zaben 2015 ba. A qasashen duniya za ka samu jam’iyya tana da tsari amma ba ta iya kafa gwamnati saboda wasu dalilai, amma yanzu babban abin da yake gabanmu shi ne a gyara PDP.