Bara da roko da maula: Sana’a ko mutuwar zuciya a al’adar Bahaushe?

Roko, bara da maula na da matukar illa ga bunkasa ci gaban duk wata al’umma.

Bara da roko da maula: Sana’a ko mutuwar zuciya a al’adar Bahaushe?

Bara aiki ne da mai yi ke nuna gazawa da kaskantar da kai, don neman taimako daga wani ko wasu don fita daga cikin wani tsanani ko rashi ko yanayi da ya tsinci kai.

Roko, nau’i ne na bara da mai yi ke neman agaji ko tallafi ko alfarma, a wurin wani ko wasu musamman wanda ya sani, domin biyan wata bukata ko samun mafita daga wani yanayi ko matsala.

Maula aiki ne da mai yi ke amfani da roko ko bara ko karairayi ko wulakanta kai da sauran dabaru, don nuna gazawa a matsayin hanyar neman abinci ko biyan bukatu na rayuwa.

Sana’a

Sana’a ita ce daukar wani aiki ko aikatau a matsayin abin yi na yau da gobe, don neman abinci ko samun abin biyan bukatu na rayuwa,

Mutuwar zuciya

Wata lalura ce da ake tsintar kai a ciki, alamominta sun hada da son jiki, lalaci, dogara da wani, rashin iya katabus ta fuskar neman na kai, karyar babu ko karyar maraici ko ta rashin lafiya, don samun tausayi da jin kai daga jama’a a kullum.

Me ke kawo bara da roko ko maula?

Allah Mai girma da Buwaya Shi ke tsarawa da rarraba arzikinSa ga kowa, yadda Yake so, ga wanda Yake so. Wani Ya ba shi da yawa wani ya ba shi kadan wani ma Ya hana shi.

A daya gefen kuma sai Allah Ya kimtsa wa dan Adam basira da hikima da lafiya, domin ya nema daga cikin arzikin Ubangiji, ta hanyar kasuwanci ko sana’a ko aiki, noma, kiwo da sauransu.

Idan muka dauki maslahar da take sa a nemi taimako ko agaji daga wajen al’umma, akwai wadanda shari’a ta aminta su nemi taimako kai-tsaye a wajen al’umma, daga cikinsu akwai wadanda Allah Ya halitta da nakasa ko suka samu nakasar daga baya, da masu yawan shekaru ko tsofaffi marasa gata da wadanda rashin lafiya ya ci karfinsu kuma babu gata da matafiyin da guzuri ya yankewa koda kuwa shi mawadaci ne a garinsu, sai kuma masu tsananin karancin abin hannu.

Amma har haka shari’a ta yi togaciya kan roko ko neman taimako inda ta yarda ka nemi taimako ko ka roki jama’a su taimaka maka, a yayin da ka shiga cikin wani tsanani domin samun mafita, kuma da zarar ka samu biyan bukata, to shari’a ta yi maka togaciya da bara ko roko ko maula.

Amma duk mutumin da ya mayar da roko ko bara ko maula aikin yi na yau da kullum, to wannan ya hadu da lalurar mutuwar zuciya. Abin tambaya da daure kai shi ne, irin abubuwan da muke gani yanzu na yawaitar roke-roke da barace-barace da maula da maza da mata ke yi.

Shin bara sana’a ce ko kawai mutuwar zuciya ce?

Idan muka duba tarihin Malam Bahaushe za mu ga cewa an san Bahaushe da azama, hazaka, juriya, kunya, kawaici da dogara da kai, domin kauce wa wulakanci a rayuwa.

Wannan ya sa Bahaushe ya shahara a harkar fatauci zuwa kasashe, har ta kai Bahaushe na iya kafa gari da alkaryu a kasashen da ba nasa ba, a sanadiyyar yawaitarsa a wurin.

Haka zalika an san Bahaushe da runguma tare da daraja sana’o’in gargajiya, wadanda ya gada iyaye da kakanni, har takan kai a gari za ka samu kowane gida da irin tasu sana’ar.

Ga kuma uwa-uba noma da kiwo, wanda gidan kowa akwai.

To wai a wancan lokacin babu talauci ne ko kuwa masu mutuwar zuciya ce babu? Shi ya sa a wancan zamanin aka samu karancin masu barace-barace ko maula?

Mai karatu zai yarda da ni cewa duk wanda ya kwana ya tashi a wannan zamani, yana ko ya taba ganin rukuni na irin wadannan mutane da zuciyarsu ta mutu da sunan mabukata ko masu rauni, maza ko mata.

Irin wadannan mutane na bin kwararo-kwararo a unguwanni da kasuwanni, musamman unguwannin mawadata.

Mafiya rinjaye daga cikin irin wadannan masu roke-roke za ka ga mata ne, cikin su akwai masu aure, sai iyayen marayu, zawarawa ma ba a bar su a baya ba.

Mai karatu na iya tambayar cewa wadannan masu auren ina mazansu?

Masu marayu ina ’yan uwan mazansu ko danginsu? Zawarawa kuma ina iyayensu ko ’yan uwansu?

Amsar ita ce, da yawansu na da wannan gata, to idan kuwa haka ne, me ke faruwa?

Iya bincike da tuntubar irin wadannan mutane da na gudanar, bayanan da na tattara su ne, wani kaso mai girma daga cikin maza a wannan lokaci sun sakar wa matansu nauyin gida gaba daya, mata suke duk mai yiwuwa wajen samun abin da za su ci da ’ya’yansu, har da shi mai gidan.

Wannan lamari shi ne dalilin fadawar wasu mata masu karancin shekaru cikin wannan dabi’a da sunan rauni ko rashi.

Wannan dabi’a da ke neman zama sana’a, ta samu karbuwa sosai kuma sai kara habaka take yi sakamakon irin samun da ake yi da ita, kuma ba tare da wata wahala ba ko fargabar karyewar jari.

Manya daga cikin abubuwan da ke kawowa da assasa yawaitar bara da maula wadda a kasar Hausa ko Hausawa kawai ta yawaita, su ne tsananin mutuwar zuciya, hassada, kyashi da rashin tawakkali da karancin taimakekeniya.

Rashin jibintar al’amuran ’yan uwanmu yadda ya kamata, mafiya yawan al’ummarmu mun rungumi akidar da-ga-ni-sai-’ya’yana.

Illolin da roko, bara da maula ke haifarwa

Roko, bara da maula na da matukar illa ga bunkasa ci gaban duk wata al’umma da ta yi sakaci mutanenta suka rungumi wannan dabi’a a matsayin sana’a.

Daga cikin su akwai:

• Tozarta martaba da kimar al’umma.

• Gazawata fuskar bunkasar tattalin arzikin al’umma.

• Dakushewar basira daga wadanda suke da wannan dabi’a.

• Yawaitar aikata manya da kananan laifuffuka da gurbacewar tarbiyya.

• Fuskantar fadawa cikin hadarin safara, dillanci da tu’ammali da miyagun kwayoyi.

• Tabarbarewar tarbiyya da karuwar ayyukan fasikanci da ayyukan masha’a.

• Bude kofar kwararowar mutanen karkara da kauyuka zuwa birane.

• Kassara duk wani tsari na gwamnati ta fuskar samar da tallafi ga masu kananan sana’o’i, ko samar da ayyukan yi.

• Fuskantar koma-baya ko mutuwar sana’o’in gargajiya.

• Karuwar marasa aikin yi.

Mafita

Samun mafita kan wannan matsala da ta addabi al’umma’armu musamman na Arewacin kasar nan, aiki ne jajawur wanda ke bukatar sa hannun kowa, kama daga kan al’ummar gari, kungiyoyi masu zaman kansu, mawadata, masarautu da uwa uba gwamnati.

Al’umma

1. Ya zama wajibi ga al’ummarmu mu fahimci cewa taimako ko taimakekeniya, ba su tsaya ga iya masu kudi ko mawadata ba.

2. Lallai ne jama’a a kowace unguwa su san cewa akwai nauyi a kansu na jan hankali da nasiha ga wadanda aka ga alamun mutuwar zuciya a tare da su don kauce wa fada wa wannan dabi’a.

Hakan zai taimaka wajen shawo kan wannan matsala, tare da dawo da martaba da kimar al’ada da addininmu, a tsakanin abokan zamanmu.

3. Mu daina shirya wa mawadatan da ke kokari tsakani da Allah, wajen taimako da agazawa masu rauni karairayi domin raba su da abin hannunsu

Kungiyoyi

1. Akwai bukatar irin wadannan kungiyoyi su dukufa wajen shirya tarurrukan wayar da kan jama’a kan illoli da matsalolin da dabi’ar bara, roko da maula ke haifarwa a cikin al’umma.

2. Koya wa matasa kananan sana’o’in dogaro da kai a lungu da sakonmu, don rage marasa aikin yi.

Mawadata

1. Akwai bukatar mawadata a cikin al’umma su ji tsoron Allah wajen fitar da zakkarsu kamar yadda shari’a ta tanada, su kuma kara rubanya kokarinsu wajen taimako da tallafa wa wadanda shika-shikan rauni ko gazawa suka bayyana a kansu, a lungu da sakon unguwannin da suke.

2. Ya kamata mawadatanmu su bijiro da wani tsari da zai sa a san yawa da hakikanin masu rauni ko gajiyayyu da ke unguwanninsu, domin fitar da tsari da taimakon da suke bayarwa zai kai ga mabukata na gaskiya.

Malamai

1. Wajibi ne malamanmu su kara jan damara tare da zage damtse wajen wa’azi, fadakarwa da nasiha ga jama’a a kan matsayar shari’a wajen dogaro da kai, tare da haramcin da ke akwai a kan mayar da roko da bara da maula sana’a ko hanyar cin abinci, da kuma irin makomar masu wannan dabi’a.

2. Haka kuma hakkin malamai ne wa’azantar da jama’a musamman maza masu iyali, kan nauyi da hakkin da Allah Ya dora musu game da iyalansu, tare da wajabtar sauke wadannan hakkoki.

Da kuma sanar da su irin narko da azabar da ke kan duk wanda yai sakaci da wannan hakki.

Sarakuna

1. Lallai ne masu rike da sarautun gargajiya, su yunkura da gaske wajen kawar da wannan dabi’a, domin dawo da kima da martabar Bahaushe da al’adarsa, mai cike da yakana, sanin ya kamata da kaurace wa abin hannun wani ko dogaro da wani.

2. Akwai matukar bukatar dagatai da masu unguwanni domin kusanacinsu da jama’a, su sanya ido kan irin wadannan mutane, domin zaburar da su kan jajircewa wajen neman na kai.

Tare da jan hankalin mawadata da ke yankunansu, wajen yawaitawa da fadada taimakon da suke yi, cikin al’umma.

Gwamnati

1. Lallai ne gwamnatocinmu musamman na Arewa, su sake shiri wajen aiwatar da ayyuka da tsare-tsare, wadanda za su sama wa jama’a sauki a rayuwarsu ta yau da gobe, su guji aiwatar da duk wani tsari da zai kuntata rayuwar talakawa.

2. Lallai ne gwammnati ta fitar da tsarin tallafa wa manya da kananan masana’antunmu hada da kyautat awa kananan sana’o’i da yanayin kasuwanci mai kyau, domin dorewa da ci gabansu.

Ta haka ne za a samar da ayyukan yi masu yawa ga al’umma, tare da rage zaman kashe wando da ke kawo bara da maula.

3. Hukumomi su kara azama wajen bunkasa samar da ilimin sana’o’i (entrepreneurship) tare da kakkafa cibiyoyin samun horo kan sana’o’i (skills acquisition centers), a unguwanni.

4. Akwai bukatar hukumomin zakka su kara kaimi wajen karbar zakka a hannun mawadata, tare da rarraba ta ga muskinai na gaskiya da kuma wadanda shari’a ta yarda a ba su.

5. Gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su sake farfado da tsarin ba da tallafi na lafiya, ilimi da sauran abubuwan wajibci na rayuwa, kamar yadda yake a baya.

Garba Nuhu Musa, Jami’in Hulda da Jama’a a Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Kasa (NOA) da ke Kano.

Marubuci ne kuma mai yin sharhi a kan al’amuran yau da kullum kuma Babban Daraktan Kungiyar Community Advocacy to Promote Sustainable Peace (CAPSP), Mamba a Kungiyar Conflict Management Mitigation Regional Council (CMMRC) za a iya samun sa ta: 08034463379.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja