Bara na mayar da ’ya’ya bayi a birane

Ba abin da nake fatan gani, kamar a ce kullum ana tafiyar da rayuwa a bisa turbar da muke sameta a baya. Domin yanzu muna bisa wata turba ce mai kama da jahiliyyar farko, jahiliyyar da har yanzu ilmi bai gusar da ita daga al’ummar mu ba. Shi yasa a kullum nake fatan a samu […]

Bara na mayar da ’ya’ya bayi a birane
Bara na mayar da ’ya’ya bayi a birane

Ba abin da nake fatan gani, kamar a ce kullum ana tafiyar da rayuwa a bisa turbar da muke sameta a baya. Domin yanzu muna bisa wata turba ce mai kama da jahiliyyar farko, jahiliyyar da har yanzu ilmi bai gusar da ita daga al’ummar mu ba. Shi yasa a kullum nake fatan a samu sauyi, irin sauyin da zai sauya dukkan rayuwarmu, ya kawo mana cigaba da bunkasa, ta yadda kananan kabilu da makwaftanmu su daina nuna mu da yatsa. Abin takaici da alhini, har yau muna nan inda muke, ba ma inda abin ya fi tsananta irin yankunan mu na karkara. Domin har yanzu sun kasa magance matsalar tura kananan ’ya’yansu birane wurin barace~barace, (wai,wurin neman ilmin addinin Musulunci).
Yawancin al’ummarmu da ke karkara har yanzu sun kasa gane cewar a yau za su iya sa ’ya’yansu a makarantun addini su samu ilmi mai kyau a gida. Lokacin hijirar neman ilmi ya wuce. Waccan hijirar da aka yi ta neman ilmin addini ta sha bamban da abin da ke faruwa a yau.
Ta yaya za a dauki yara kanana ’yan kasa da shekara bakwai a kai su wani gari da sunan karatun addini, ba tare da an san abin da yake faruwa da su ba, da kuma halin da su ke ciki? Yaran da ake turawa birane, an san ba karatu suke zuwa nema ba, saboda kodayaushe za ka same su ne a tashoshin motoci suna bara, sun mayar da bara ta zama sana’a arsu. Sun saba dole sai wani ya ci ya rage musu sannan za su ci, sannan za su iya biya wa kan su bukatun rayuwa.
Ta wace hanya ake jin yaro zai yi tunanin bari ya tashi ya dogara da kan sa, ko kuma ya yi tunanin yin wani abu da zai zama a gaba, ya nemo wa al’ummarsa garkuwa? Bayan ya taso zuciyar sa a makance, ba ya iya neman na kansa, ta yadda hatta abin da zai ci ya saba sai wani ya ci ya rage masa.
Addinin Musulunci bai koyar da mu irin wannan rayuwa ta barace-barace ba, ana dai fakewa ne da sunan addini kawai ana tura yara kanana wasu garuruwan; wasu mutane suna ciyar da su, bayan kuma mun sani cewa iyaye Allah (S.W.A) ya dora wa nauyin tarbiyar ’ya’yansu ba al’umma ba.
A yau ba wani gari komai kankantarsa a garuruwanmu na Musulunci da za a ce babu masu ilmin addinin da za su bude makarantu, su koyar da yara, su ba su karatu mai kyau da tarbiya. Sai dai saboda son rai da neman sauki da rashin kulawar  wasu iyaye ga makomar ’ya’yansu, da an cire yaro daga nono za su fara tunanin garin da za su kai shi ya yi bara. Wasu sai su shekara biyar ba su je sun ziyarci ’ya’yansu sun ga halin da suke ciki ba, sai dai ’ya’yan ne suke sayen sutura wani lokaci su aika wa iyayensu, kuma su amsa suna murna, suna sa musu albarka. Sun mayar da ’ya’yansu bayi a wasu garuruwa.
A haka har suna iya fitowa su ce “gwamnati azzaluma ce, shugabanni ba su da adalci”, a haka za mu samu shugabanni masu tausayi? Bayan su ba su ji tausayin hatta ’ya’yan cikinsu ba? Wadannan ’ya’yan da ire-iren su da iyayensu suka mayar bayi, su ya kamata a yi amfani da su wajen gina yankunansu, maimakon mayar da su bayi a cikin birane.
Rashin kulawar  wasu iyaye ga ’ya’yansu, ita ce ummul haba’isin duk wani tashin hankalin da ke faruwa a kasar nan. Yaya amana ce a wurin iyayensu. Akan me Allah ba zai jarrabe mu ba? Akan me Allah ba zai kawo tashin hankali ba? Bayan anyi watsi da amanar da ya dora mana. Idan ba mu dawo mun gyara tsakaninmu da Allah ba, mun kaunaci juna ba, mun daina kyashin juna ba, mun gyara kura-kuran mu ba…to za a wayi gari wata rana mun zama tarihi. kamar yadda wani ya yi ikirari).
’Ya’yanmu ba bayi ba ne, hakki ne day a rataya a kanmu,mu ilimantar das u, mu ba su tarbiyya ta gari,don kada su zama nauyi ga al’umma.
Idan kana kuka ba ka daga murya ba, ba mai jin ka. Saboda haka dole ne mu koyi fitowa muna fadar gaskiya, muna fadar abubuwan da su ne damuwar mu, domin samun sauki. Mu farga, mu farka ’yan Arewa.

Bashar Bello Alkali
Sokoto Cinema Jahar Sakkwato 07063691636.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya