Bara’a ce maganin azzaluman Najeriya

Kowa ya san shugabancin Najeriya, musamman Soja da PDP sune suka jefa mu halin da muke ciki yanzu, amma saboda rauni hatta wasu daga cikin malaman addini da ‘yan boko da sarakuna da attajirai da ‘yan siyasa duk sun zuba ido tamkar da su aka hada baki ake yin duk satar da ake yi mana, […]

Bara’a ce maganin azzaluman Najeriya
Bara’a ce maganin azzaluman Najeriya

Kowa ya san shugabancin Najeriya, musamman Soja da PDP sune suka jefa mu halin da muke ciki yanzu, amma saboda rauni hatta wasu daga cikin malaman addini da ‘yan boko da sarakuna da attajirai da ‘yan siyasa duk sun zuba ido tamkar da su aka hada baki ake yin duk satar da ake yi mana, ta mutane da dukiya da kisa da tsafe-tsafe da kowanne fajirci nasabawa Allah. Talakawa da abin ya fi cutarwa sun kasa haduwa su ce ba su yar da ba. Satar daruruwan ‘yanmata da matan aure da yankan rago da ake ta yi wa dalibai da magidanta; ga satar kudin gurbataccen mai da hana talakawa yin zanga-zangar lumana, sai malaman jami’o’i, da ma’aikata: Likitoci da ungozomomi. Duk wadannan ba sa tunanin masu mulki, na da dama yanzu kowannensu ya ci gaba da sharholiyar da yake yi, na fajirci da tsafi da kisa da sata da shaye-shayen ababen sa-maye da haukatarwa.
Shi yasa hukunta masu laifi ba zai yiwu ba, kamar yadda na sha fadi duk abin da aka yi a hana  ya ki hanuwa, to masu ikon hanawar ne ke yi. Su ke gurbata ‘yan baya (matasa) samari da ‘yan mata. Al’umma ta fada wani hali na halaka, sai abin da Allah ya yi, idan har ba mu iya kawar da masu saba wa Allah daga mulki da shugabantar al’umma ko jagoranciba. Musamman da ake samun limaman addini da laifin lalata yara, maza da mata da mata naure. Abin ya watsu har a jami’o’i da makarantun kwana. An kasa hana wa saboda an kasa yi musu hukuncin da Allah ya ce ayi musu a bainar jama’a. Yanzu an zo makura ko dai masu ikon gyarawar su gyara, ko mu dauki mataki akan su gaba daya, tare da abokan yin nasu.
Gyara yana farawa ne daga mutum daya, amma ba aikin mutum daya tilo ne ba.
Kamar yadda barna ba ita ta yi kanta ba, haka ma gyara ba zai yi kansa ba. Tilas sai wasu ma’abota gyara sun hadu  sun gyara, ko a gamu da fushin Allah, irin yadda muke fama da annobar mutuwa a halin yanzu.
Idan shugabanni suka lalace, me ya kamata mu mabiya mu yi? Mu yi musu bara’a! Duk wanda ka ga ni cikin inuwa wasu ne suka tsaya masa a rana. Bara’a ce maganin azzaluman shugabanni. Wayo, yasannaki! Idan suka ce –e,  mu ce  ‘a’a’, idan suka ce wayo – mu ce mun ki! Allah ya sa mu gane, mu yi riko da igiyar Allah kada mu rarrabu. Allah ya sa mu ne za mu gyara komai ameen, summa ameen. Allah ba zai canza mana ba, har sai mu da kanmu mun canza; mun daina aikata zunubai, mun tuba ga Allah tuba na hakika, ba tuban muzuru ba. Kowa yaki ji, ba zai ki gani ba!
Mu tuna Allah ya ce, mafiya yawan mutane ba su da hankali, mafiya yawan mutane ba su sani ba. Duk wanda yake da hankali, ya kuma san ibai kamata ya daka ta mafiya yawa da Allah ya ce ba su sani ba, ko ba su da hankali. Ina hankali ga shugabannin da za su sace dukiyar kasar da suke mulkinsu kai wasu kasashe su boye, wai can ya fi tsaro, yayin da su da ‘ya’yansu da matansu har da iyayensu suke ciki rashin tsaro?
‘Yan jarida na kwarai su suka fi dacewa da isar da sakonnin mutanen kirki na samar da juyin-juya-hali (cultural rebolution) ga sauran al’umma baki daya. Kwatankwacin irin yadda sahabbai suka rika samun sakonni daga Annabi (S.A.W) suna isar wa ga al’umman a ko’ina, birane da kauyuka a zamaninsu, wannan shi ne cikakken misali. Annabin Allah da Allah yake aiko mala’ika gareshi sai da sahabbai suka taimaka masa wajen isar da sakon Allah, saboda haka Allah ya tsara, da Allah ya ga dama ba sai wani ya taimaki Annabi ba zai samar da canji ga rayuwar al’ummar duniya.
Bin nagaba, bin Allah
Ana bin nagaba idan nagaban yana kan bin Allah (S.W.T), domin Allah shi ne abin bi nagaskiya. Masu kira da a rika yi wa shugabanni biyayya suna mantawa da yin kira ga shugabanni da suka san ce masu bin Allah da Annabin Allah, matukar suna so ayi musu biyayya. Kada su kasance barayi, fajirai, matsafa, azzalumai da makamantansu. Aikata laifuka irin wadannan shi yake jawo annoba iri-iri.  Allah ya fi kowa kishi! Duk wanda ba ya bin umarnin Allah, koda dansa ya yi wa umarni ba zai bi umarnin ba, ya kamata kowa yasan wannan. Shugabanni su ji tsoron haduwa da fushin Allah, su kiyaye umarnin Allah, su yi adalci tsakanin kowa da kowa, ba tare da kowanne irin bambanci ba. Idan shugabanni basa bin umarnin Allah, sai aki bin umarninsu, abin da Allah. Masu kira da a yi wa shugabanni addu’a, su rika yi wa shugabannin nasiha – kada su yi zalunci da fajirci da kisa da sata da karya ko yaudara.

Alhaji Abdulkarimdaiyabu
ShugabanRundunarAdalci ta Najeriya-
Mobement for Justice in Nigeria (MOJIN),
08060116666, 08023106666

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya