baraka ta kunno kai a PDP reshen Jigawa
baraka ta kunno kai a Jami’yyar PDP reshen Jihar Jigawa, sakamakon batun zaben Shugaban kasa a badi.Wadansu daga cikin ’ya’yan Jam’iyyar PDP mai mulkin a Jihar Jigawa da ke goyon bayan sake tsayawa takarar Shugaba Goodluck Jonathan ne suka fara mayar da martani kan kalaman da Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya yi cewa shi […]
baraka ta kunno kai a Jami’yyar PDP reshen Jihar Jigawa, sakamakon batun zaben Shugaban kasa a badi.
Wadansu daga cikin ’ya’yan Jam’iyyar PDP mai mulkin a Jihar Jigawa da ke goyon bayan sake tsayawa takarar Shugaba Goodluck Jonathan ne suka fara mayar da martani kan kalaman da Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya yi cewa shi da magoya bayansa ba za su bi Shugaba Jonathan ba idan ya yanke shawarar tsayawa takara a zaben badi, matukar bai cika wa jihar alkawuran da ya yi mata a bay aba.
Gwamna Sule Lamido ya ce gabanin zaben shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa al’ummar jihar alkawarin wasu ayyuka domin su mara masa baya, amma har yanzu ba a cika musu ko da daya daga cikin wadannan alkawura ba, don haka al’ummar jihar ba za su sake goya masa baya ba.
Sai dai tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar, Alhaji Abba Anas Adamu ya shaida wa manema labarai a Dutse cewa suna goyon bayan takarar Shugaba Goodluck a zabe mai zuwa, kuma Gwamna Sule Lamido yana magana ne kawai a madadin kansa ba al’ummar jihar ba.