Barau ya buƙaci Ganduje ya ƙwato wa APC ƙarin jihohi

Barau ya ce jam’iyyar na sa ran samu wasu nasarori a ƙarƙashin jagorancin Ganduje.

Barau ya buƙaci Ganduje ya ƙwato wa APC ƙarin jihohi

Barau I. Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, bisa ƙoƙarinsa na tallafa wa jam’iyyar APC.

Ganduje, ya zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a ranar 3 ga watan Agustan 2023, yayin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Rahotanni sun ce Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne, ya zaɓe shi don ba shi wannan muƙamin.

Duk da haka, zamansa shugaban jam’iyyar ya haifar da cece-kuce, inda wasu suka nemi ya yi murabus.

A saƙon taya murna da ya aike wa Ganduje na shekaru 75 a duniya, Sanata Barau, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashiru, ya bayyana nasarorin da Ganduje ya samu.

Ya ce APC ta lashe zaɓen gwamna a jihohin Edo, Ondo, Kogi, da Imo a ƙarƙashin jagorancinsa.

Barau, ya bayyana Ganduje a matsayin “wanda ke kawo sauyi” tare da jaddada muhimmancin hangen nesansa da gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban Najeriya.

Ya ce, “Kamar yadda na hango lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka, nasarorin APC sun ƙaru a ƙarƙashin jagorancinsa. Shi ne wanda ya kawo sauyi.

“A ƙarƙashinsa, mun lashe zaɓuka huɗu daga cikin biyar da aka gudanar a jihohin Kogi, Imo, Edo, da Ondo.

“Wannan ya samo asali ne daga kyakkyawan jagoranci, goyon bayan da yake bai wa ‘ya’yan jam’iyya, da kuma jajircewarsa.

“Kasancewarsa shugaba, muna sa ran samun wasu nasarori a jam’iyyarmu mai girma, in sha Allah.”