barawo ya aike wa mai wayar iphone da ya sata da shafi 11 na sunaye abokan huldarsa

Wani barawon wayar ‘iphone’ a kasar Sin, ya rubuto shafuka 11 masu dauke da sunayen mutum kusan dubu, sannan ya aika wa asalin mai na’urar da ya sata, kamar yadda Jaridar Hindustan Times ta ruwaito.Rahoton ya bayyana cewa dan sanen ya saci wayar ne daga hannun Zou Bin, a lokacin da suke tafiya a motar […]

barawo ya aike wa mai wayar iphone da ya sata da shafi 11 na sunaye abokan huldarsa
barawo ya aike wa mai wayar iphone da ya sata da shafi 11 na sunaye abokan huldarsa

Wani barawon wayar ‘iphone’ a kasar Sin, ya rubuto shafuka 11 masu dauke da sunayen mutum kusan dubu, sannan ya aika wa asalin mai na’urar da ya sata, kamar yadda Jaridar Hindustan Times ta ruwaito.
Rahoton ya bayyana cewa dan sanen ya saci wayar ne daga hannun Zou Bin, a lokacin da suke tafiya a motar tasi guda, a tsakanin unguwannin Yiyang da Chaugsha da ke tsakiyar gundumar Hunan.
Tunanin cewa, watakila ba shi da ajiyayyen sunayen mutanen da yake hulda da su, sai barawo ya aike wa Zou da rubutattun sunaye da lambobin mutanen da ke cikin wayarsa, don gudun kada ya shiga damuwa.
“Ina sane da cewa kai ne mutumin da ya zauna kusa da ni. Ina da tabbacin zan iya ganoka,” kamar yadda yake kunshe a sakon da ya aike wa asalin mai wayar, wato Zou. Shi kuwa sai ya aike masa da wani sako cewa: “Ka duba jerin sunayen mutanen da nake hulda da su, don za ka fahimci sana’ata, kuma tabbas sai na ganoka. Ka dawo min da wayata ta adireshina da na aiko maka, in kana da hankali.”
Zou dai ma’aikacin hukuma ne da ke lura da tsagerun mutane. Barazanar da Zou ya yi ta yi tasiri, domin ya samu sakon babbar ambulan dauke da layin wayarsa, tare da shafi 11 na rubutattun abokan huldarsa da ke cikin wayar.
“Za a dauki lokaci wajen yin wannan rubutu, inda na jera su daya bayan daya, har mutum kusan dubu, na tabbata yanzu hannun barawo ya kumbura,” inji Zou

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan