barawo ya bayar da lambar wayarsa kafin ya yi sata
Wani barawo a bihar ta kasar Indiya, ya bayar da lambar wayarsa ga wani babban jami’in gwamnati kafin ya shiga gidansa ya yi masa sata. Al’amarin ya auku a makon da ya wuce ne lokacin da barawo ya ziyarci gidan jami’in hukumar, inda ya nuna masa cewa shi limamin addinin Hindu ne, kuma mabiyin Guru […]
Wani barawo a bihar ta kasar Indiya, ya bayar da lambar wayarsa ga wani babban jami’in gwamnati kafin ya shiga gidansa ya yi masa sata. Al’amarin ya auku a makon da ya wuce ne lokacin da barawo ya ziyarci gidan jami’in hukumar, inda ya nuna masa cewa shi limamin addinin Hindu ne, kuma mabiyin Guru Sai Baba na Shirdi. A lokacin da suke tattaunawa da bakon sai ya ba shi lambar wayarsa, ya kuma bukace shi da ya ziyarci dakin ibadarsa da ke Shirdi, inda ya ce nan ne mzauninsa.
Da jami’in gwamnatinn ya ji dadin mu’amala da jabun limamin addini, sai ya shirya musu kalaci, inda daga bisani bakonsa ya bukaci ruwan sha. Da shigarsa dakin girki, don debo ruwa, sai bakon ya yi hanzari, ya kwashe sarkokin zinari da ke kan teburin dakinsa, sannan ya arce. Kayan da aka sata sun hada da sarkar zinari da zobba da zobba biyu na azurfa.
Nan da nan wannan jami’in gwamnati ya tuntubi barawon ta wayar salularsa game da satar da aka yi masa. A lokacin da suke tattaunawa, wanda ake zargi da wannan sata, ya tabbatar da cewa shi ya sace kayan, sannan ya dauki alkawarin dawo da kayan da ya sata. Ganin cewa bai dawo da kayan ba, har zuwa Litinin din da ta gabata, sai kawai ya kai kara wurin ’yan sanda.
Har yanzu jami’an ’yan sanda ba su samu nasarar kama barawon ba, balanta a samu kayan da ya sata.