Barawo ya dawo da babur din da ya sata yana rokon gafara
Yaya aka yi aka sace maka babur dinka? Ranar Lahadi (17 ga Satumba) da Magariba bayan na ajiye babur dina a cikin gidanmu mun shiga masallaci yin Sallar Magariba kafin mu idar da Sallah sai aka shiga cikin gidan aka sace min babur di. Da muka fito daga masallaci sai filin da na ajiye babur, […]

Yaya aka yi aka sace maka babur dinka?
Ranar Lahadi (17 ga Satumba) da Magariba bayan na ajiye babur dina a cikin gidanmu mun shiga masallaci yin Sallar Magariba kafin mu idar da Sallah sai aka shiga cikin gidan aka sace min babur di. Da muka fito daga masallaci sai filin da na ajiye babur, sai muka shiga cigiya ta ko’ina amma ba mu same shi ba.
Kun kai rahoto ga ’yan sanda?
Eh, washegari da safe muka je muka fada wa ’yan sanda suka ce in Allah ya so za a samu, za su yi kokari su bincika mana. Haka dai muka yi ta kokari har lokacin da Allah ya gajarta wahalanmu.
Lokacin da aka dauke babur din da kuma lokacin da aka dawo da shi yaya ka ji a ranka?
Gaskiya ban ji dadi ba da aka sace babur din, musamman wannan yanayin da ake ciki. Na shiga cikin tashin hankali domin a gasakiya ban san yadda zan yi in maida babur din ba. Haka na bar wa Allah al’amarinSa na ce, Allahn da Ya ba ni, Shi zai sake ba ni wani, abin ya daga mini hankali ba kadan ba gaskiya. Da aka dawo da babur din na ji dadi kwarai da gaske, na yi farin ciki matuka saboda abin da ka debe tsammaninsa ne aka dawo maka da shi. Kuma na tausaya wanda ya saci babur din domin har addu’a muka yi masa.
Bayan sace babur din ko akwai matakin da kuka dauka ta fuskar addu’a?
Eh, mun yi ta yin addu’o’i, kuma mun koka wa ’yan uwa da abokan arziki da malamanmu muka yi ta fada musu su taya mu da addu’ar Allah Ya bayyana mana babur din, kuma tun a daren aka satar muka yi ta yin addu’o’i. Allah Ya karbi addu’o’inmu Ya tausaya mana Ya sa aka dawo da shi. Mun yi addu’o’i da yaw sosai ba kadan ba.
Yaya aka yi aka dawo maka da babur din?
Na sallama komai na bar wa Allah, bayan kwana 12 da sace babur din sai muka ji barawon babur din ya yi sallama. Cikin ikon Allah Ya dawo mini da babur din da kansa, yana rokona gafara, ya ce in gafarta masa laifin da ya yi mini.
Ko ya fada maka dalilin da ya sa ya sace maka babur din?
Bai dai fadi wani dalili ba, illa dai ya ce mana shi dama yana sace-sacen babura kuma da ya dauki wannan shi ne ya dawo da shi.
Wane dalili ne ya ce ya sa ya dawo da shi?
Ya ce tun ranar da ya saci babur din har ranar da ya dawo da shi ba ya da kwanciyar hankali, ya kasa zaune ya kasa tsaye ko barci ba ya iya yi. Shi ne ya sa ya ce bar ya dawo da shi ya ba da hakuri, kuma ya roki gafarana. Ya ce kuma shi ma ya roki Allah Ya gafarta masa Ya yafe masa Ya shiryar da shi, ya fi karfin zuciyarsa domin shi ma ya ce a dole ne yake yin haka.
Bayan da ya kawo babur din ko akwai wani mataki da kuka dauka a kansa?
A’a mutum ne ya yi maka laifi, ya dawo da shi kuma ya roke ka gafara ya ce ka yafe masa, yana neman Allah Ya yafe shi, yaya za ka yi kuma ka kai shi ga hukuma? Tunda ya yi nadama ai sai ka yafe masa bayan mun yafe masa ma sai da muka yi ta yi masa addu’o’i muna rokon Allah Ya buda masa ko zai samu na kansa ya daina wannan mummunar sana’a.
Matsalar sace-sacen babura matsalace da kullum take faruwa a nan Bauchi ko ka lura da haka?
Eh, gaskiya na lura da haka sosai, domin ko ranar da aka sace mini babur dina an dauki na wani a titin Bakin Kura shi ma suna Sallar Magariba, cikin makon kawai na ji labarin an saci babura akalla guda biyar.
Me za ka ce game da kokarin da hukuma ke yi don magance sace-sacen?
Gaskiya suna kokari sosai sai dai mu yi fatan Allah Ya taimake su su gane miyagun da suke aikata wadannan laifuffuka su kama su. Gaskiya hukuma tana kokari kwarai da gaske domin da muka yi rahoto sun nuna damuwarsu sosai a kan lamarin ba sosai ba.
A karshe wace shawara za ka bai wa masu babura?
Shawarar da zan ba masu babura ita ce su kara kula da baburansu, tunda yake Allah Ya sa akwai hanyoyi da ake bi a kulle babur din musamman ta hanyar yin amfani da kwadunan da ake sanyawa ta kasa, duk mutumin da ya sayi babur ya yi kokari ya sa kwadon kasa. Kuma kada mutum ya raina ’yan mintocin da zai yi in ya rufe babur din, duk inda ya tsaya ya tabbata ya sa kwado ya kulle daga kasa, domin yawanci masu satar babur in dai suka leka suka ga wannan kwado daga kasa ba sa iya dauka. Ko dakika goma mutum zai yi a wuri to ya kulle daga kasa, insha Allahu zai dawo ya samu babur dinsa.