barawo ya kone wanda ya yi wa sata

Wani matashi mai suna danmaraya da ake zargi da sata, ana kuma zarginsa da watsa wa wanda ya yi wa satar mai suna Muhammad Nura Sulaiman da ke zaune a kauyen Dokar danbala a karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna man fetur sannan ya cinna masa wuta, wanda haka ya yi sanadin rasuwarsa.  Wanda ake […]

barawo ya kone wanda ya yi wa sata

Wani matashi mai suna danmaraya da ake zargi da sata, ana kuma zarginsa da watsa wa wanda ya yi wa satar mai suna Muhammad Nura Sulaiman da ke zaune a kauyen Dokar danbala a karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna man fetur sannan ya cinna masa wuta, wanda haka ya yi sanadin rasuwarsa. 

Wanda ake zargin ya babbake marigayin ne bayan ya yi masa sata a shagonsa har sau biyu, kuma lamarin ya faru ne cikin dare a ranar Alhamis din makon jiya.
Da yake yi wa wakilinmu bayani kan yadda lamarin ya faru, mahaifin marigayin Alhaji Ayuba Sulaiman ya ce, “Ina cikin gida ina kwance da misaln karfe 11:00 na dare a ranar Alhamis, sai na ji ihu a waje ana cewa wuta! Wuta! Sai na tashi a birkice na fito inda na hadu da marigayin a kofar gida, sai ya ce, mini “Baba, danmaraya ne ya kona ni. Tun da na ga irin konewar da dukkan jikin marigayin ya yi, sai hankalina ya tashi na tsorata kan makomar rayuwarsa. Daga nan sai na koma cikin gida na rasa abin da yake yi min dadi, na fadi kasa saboda rudewa.”
Ya kara da cewa: “Ita ma mahaifiyar marigayin da ta ga halin da yake ciki sai ta fadi. Daga nan muka dauke shi zuwa wani asibiti a garin Unguwar Bawa da suka ga halin da yake ciki sai suka ce abin ya fi karfinsu.”
Alhaji Ayuba ya ce daga nan suka wuce zuwa wani asibiti a garin Jingir da ke Jihar Filato, nan ma suka ce abin ya fi karfinsu sai dai su wuce zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) da ke garin Jos.
Ya ce da suka ji haka sai suka dawo da shi zuwa asibitin da suka fara zuwa a garin Unguwar Bawa, ya ce da gari ya waye suka ga halin da yake ciki, sai muka yanke shawarar dawowa da shi zuwa gida domin a yi masa maganin gargajiya. “Da muka dawo gida a safiyar ranar Juma’a ba mu dade ba ya rasu,” inji shi.
Alhaji Ayuba Sulaiman ya ce a kullum idan marigayi ya tashi daga shagonsa yana zuwa ya zauna a kusa da kofar gidansa ya huta kafin ya shiga gida. Ya ce a wannan rana bayan ya tashi kamar kullum, sai danmaraya ya zo ya same shi, ya watsa masa fetur ya kunna masa wuta. Ya ce da aka zo kashe masa wutar ne bayan ta cinye kayan jikinsa, shi ne yake fadin cewa danmaraya ne ya kona shi.
Ya ce yaron da ya yi aika-aikar mahaifiyarsa ce ’yar garin, amma mahaifinsa mutumin kauyen ’Yar Maraya ne a karamar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano.
“Wannan yaro ya fasa shagon marigayin ya yi masa satar kaya har sau biyu da aka kama shi sai marigayin ya ce ya yafe saboda ganin muna makwabtaka da kakanninsa, aka bar maganar ba a yi masa komai ba. Da wannan abu ya faru sai yaron ya gudu daga garin ya koma wurin mahaifinsa. Bayan kamar kwana 70 ne ya dawo ya aikata wannan mummunan aiki,” inji shi.
Shi ma da yake zantawa da wakilinmu shugaban matasan kauyen Malam Gambo Ibrahim Dokar danbala ya nuna takaicinsa kan faruwar lamarin.
Ya ce yaron da ya aikata wannan laifi, sau biyu yana yi wa marigayin sata a shagonsa, amma ya yi hakuri ya bar shi bai dauki wani mataki ba a kansa.
Ya ce wanda ake zargin ya baro wurin mahaifinsa ne ya taho kauyen ya ce zai zo ya yi noman rake. “Ya zo a cikin dare ya samu marigayin ya rufe shagonsa yana hutawa, sai ya watsa masa fetur ya cinna masa wuta,” inji shi.
Ya ce da safe ’yan uwan marigayin suka fita suna neman wanda ake zargin, sai suka kama shi yana tafiya a kafa a tsakanin wannan kauye da kauyen Agaji. Da aka kamo shi sai aka mika wa ’yan banga su kuma suka mika wa sojoji su ma suka mika wa ’yan sanda.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Zubairu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce tuni an kama matashin da ake zargi da wannan danyen aiki, kuma ana ci gaba da bincike a sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar.