barawo ya saci takalman mata 450

An kama wani barawo a kasar Japan da ke zuwa kulob-kulob din shakatawar mata ya sato takalmi mai tsini, da jami’an ’yan sanda suka bincika dakinsa sun samu takalmi kafa 450.“Ina samun nishadi a satar takalmi mai tsini. Ba kuma na sha’awar sababbin takalma,” a cewar barawo Sho Sato, dan shekara 28, kamar yadda ya […]

barawo ya saci takalman mata 450

An kama wani barawo a kasar Japan da ke zuwa kulob-kulob din shakatawar mata ya sato takalmi mai tsini, da jami’an ’yan sanda suka bincika dakinsa sun samu takalmi kafa 450.
“Ina samun nishadi a satar takalmi mai tsini. Ba kuma na sha’awar sababbin takalma,” a cewar barawo Sho Sato, dan shekara 28, kamar yadda ya bayyana wa masu bincike da suka kama shi.
Sato dai mara aikin yi ne, kuma ba shi da wurin kwana, ya kuma shiga dakin shakatawar mata  kulob din Glitzy da ke birnin Tokyo a gundumar  Ginza, cikin watan Nuwambar bara, inda ya saci takalmi kafa 14 da kayan shafe-shafen kwalliyar mata, a cewar ’yan sanda.
An kuma kwace takalami kafa 450 masu tsini, a wani daki da ya kama haya, amma har yanzu ba a gano wanda ya mallaki dakin da ya kama ba.