Barawo ya saci warin takalmi kafar dama 13
Rob Wickham wanda ke da kantin sayar da kayayyakin sanyawa a Jihar birginia ta kasar Amurka ya ce, an kama mutum biyu da suke fasa kantinsa suna yi masa sata shekara biyu da suka gabata a ranar 20 ga Yuli da 25 ga Agusta 2018. Wickham, ya ce, ya rasa takalma warin kafar dama sau […]
Rob Wickham wanda ke da kantin sayar da kayayyakin sanyawa a Jihar birginia ta kasar Amurka ya ce, an kama mutum biyu da suke fasa kantinsa suna yi masa sata shekara biyu da suka gabata a ranar 20 ga Yuli da 25 ga Agusta 2018.
Wickham, ya ce, ya rasa takalma warin kafar dama sau ciki lokacin hutu da ake yi na shekara inda aka rufe kantin sau biyu don yin hutu.
A daidai lokacin hutun an yi satar kayyakin kantin wadanda suka hada da: riguna da wanduna da rigunan sanyi da warin takalma sau ciki guda13.
Wickham ya ce, ya kasance yana fito da warin takalma na kafar dama don tallata wa mai saye a kofar kantin, wadannan barayin ba su yi sa’ar abin suka kwasa ba.
Kakakin ’Yan sandan yankin Roanoke, Amy Whittaker ya ce, a watan Yuli sun tsare wani dan shekara 17 da ake zargi da fasa tagar kantin, yayin da ’yan sandan suka fitar da shaidar faifan bidiyo da ke nuna lokacin da wanda ake zargi ya fasa taga yana yunkurin yin sata.