Barawon akuya ya kade ’yan acaba uku a Kwara

Lamarin ya faru ne a Unguwar Akerbiata da ke Ilorin ta Kudu a Jihar Kwara

Barawon akuya ya kade ’yan acaba uku a Kwara

Akuya

Wani mai mota da ake zargi da satar akuya ya shiga hannu ’yan sanda bayan da ake zarginsa da kade wasu ’yan acaba su uku a kokarinsa na tserewa.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Akerbiata da ke Ilorin ta Kudu a Jihar Kwara a farkon makon nan.

Mai akuyar da aka sace mai suna Iya Kehinde Eleran ta shaida wa wakilinmu cewa, ’ya’yanta da suke neman akuyar ce suka gan ta a wurin wanda ake zargin mai suna Isiaka yana kokarin jan hankalinta don shiga motarsa, su kuma suka yi kokarin jawon hankalin jama’a domin a hana shi.

“Ganin haka sai ya tura akuyar a cikin motar kirar Toyota mai launin toka, ya shiga ya zabura da gudu, daga baya muka ji cewa ashe motar ma ta sata ce.

“Sai ‘ya’yan nawa suka bi shi sun ihu barawo! barawo!! A kokarinsa na tserewa sai ya kade wasu ’yan acaba su uku, hakan ya fusata ’yan uwansu, suka bi shi don kama shi,” in ji ta.

Ta ce daga karshe ya shiga hannu, mutane kuma suka yi kokarin kone shi, amma zuwan ’yan sanda ya sa ya tsira da ransa.

 

Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja

MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP

Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas

Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo