barawon awaki ya shiga a hannu a Binin

barawon awakin mutane ya shiga hannu, inda a Talatar makon jiya ya saci awakin wata mata mai suna Mama Kenneth a Unguwar Uselu cikin garin Benin jihar Edo. Wanda ake zargin mai suna Omogiabia Edwien mai kimanin shekaru 50 a duniya yace yana da matan aure daya tare da yara biyar kuma yana zama ne […]

barawon awaki ya shiga a hannu a Binin
barawon awaki ya shiga a hannu a Binin

barawon awakin mutane ya shiga hannu, inda a Talatar makon jiya ya saci awakin wata mata mai suna Mama Kenneth a Unguwar Uselu cikin garin Benin jihar Edo. Wanda ake zargin mai suna Omogiabia Edwien mai kimanin shekaru 50 a duniya yace yana da matan aure daya tare da yara biyar kuma yana zama ne a Unguwar Akiadolor da shi da abokin barnarsa mai suna Ozigbe wanda yake shi direba ne na tasi.
A babbar kasuwar dabbobi ta Benin aka kama barawo da wata karamar mota, tare da wani abokinsa Ozigbe, sai ya sauka da wani kunshin wake ya zuba wa awaki da tumaki, nan take ya buge wata akuya ya jefata cikin mota, sai ya rarumi akuyar tare da wata uwar tumkiya, Omogiabia Edwien yana cikin wannan aika-aika ido rufe, yana cusawa cikin wannan motar, sai mutane suka ankara lallai shi barawo ne, sai suka labarta wa Shugaban ‘yan Banga na kasuwar, Shuaibu Muhammed, nan da nan sai ga  su suka dira akan wadannan barayin.  Suka fara fafatawa da su, har suka kama Omogiabia Edwien, amma abokinsa ozigbe tuni ya  ranta ana kare, ba a samu an kama shi ba.
Jami’in ’yan sanda DPO,. na shiyyar Mista S.Obiuwebbi ya tabbatar da kama wanda ake zargin, kuma ya ce ‘’Mai laifin  mun karbe shi daga hannun ’yan banga da suka kawo mana shi. A cewarsa, yana tsare a wurinmu har sai mun kammala bincike akansa, kafin  mu mika shi ga kotu’
’Domin akwai bukatar samun kama abokin aikinsa, wanda aka ba mu labarin ya gudu ba a samu an kama shi ba, kuma da matar nan Mama kenneth da ya ce ita ce yake kai wa dabbobin da yake sata na jama’a yana sayar mata kimanin shekaru biyar,” inji shi.
Jami’in ’yan sandan shiyyar,  Mista S.Obiuwebbi, ya bayyana cewa ‘’Mai laifin yana bada hadin kai, amma ba a gama gano komai ba, duk da cewa ya tabbatar mana da ya aikata wannan laifin da ake zarginsa da shi.’