Barawon da ya bugar da mai Keke NAPEP ya sace ya shiga hannu a Kano
’Yan sintiri a Qaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano sun kama wani matashi mai suna Bashir Musa da ke zaune a Kurna, Layin Gidan Kara bisa zarginsa da qwacen Keke NAPEP da aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ bayan ya shaqa wa direban wani sinadari, wanda ya yi sanadiyyar batar da hankalinsa. Aminiya […]
’Yan sintiri a Qaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano sun kama wani matashi mai suna Bashir Musa da ke zaune a Kurna, Layin Gidan Kara bisa zarginsa da qwacen Keke NAPEP da aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ bayan ya shaqa wa direban wani sinadari, wanda ya yi sanadiyyar batar da hankalinsa.
Aminiya ta gano cewa, duk da cewa bayan Bashir ya sace motar kuma ya canja mata fenti da lamba, hakan bai hana ’yan uwan direban gane ta ba, wanda hakan ya sa suka sanar da ’yan sintirin halin da ake ciki.
Aqibu danlami shi ne Kwamandan ’Yan sintiri na Qaramar Hukumar Dala, ya bayyana wa Aminiya cewa bayan ’yan uwan direban sun sanar da su halin da ake ciki, sai suka kama motar a hannun wanda ake zargin tare da neman ya kawo musu takardunta, inda ya gaza bayyana su.
Malam Aqibu ya ce za su hada kai da ’yan sanda domin fadada bincike a kan lamarin tare da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Wanda ake zargin, Bashir Musa wanda ya a baya ke sata da dillancin awakin sata, ya bayyana yadda ya samu nasarar qwace babur din na Keke NAPEP daga hannun direbansa kamar haka.
“Wannan ne karo na farko da na fara wannan harka, domin ni barawon awaki ne a da, wanda hakan ya sa aka kai ni kurkuku. Kuma a can ne na hadu da wani abokina mai suna Adamu; wanda shi ya nuna min wannan harkar har ma ya taimaka min wajen qwace Keke NAPEP din daga hannun direbanta,” inji shi.