barawon jakar mata ya shiga hannu

Dubun wani barawon jakunkunan mata mai suna Musa Abubakar Gwandara ta cika a yayin da ya yi kokarin kwace wa wata mata jakarta a wani lungu cikin anguwa kusa da babbar kasuwar dabbobi ta garin Benin, Jihar Edo.barawon, wanda ya kai kimanin shekaru 25 da haifuwa, an shaida cewa ya dade yana yi wa matan […]

barawon jakar mata ya shiga hannu
barawon jakar mata ya shiga hannu

Dubun wani barawon jakunkunan mata mai suna Musa Abubakar Gwandara ta cika a yayin da ya yi kokarin kwace wa wata mata jakarta a wani lungu cikin anguwa kusa da babbar kasuwar dabbobi ta garin Benin, Jihar Edo.
barawon, wanda ya kai kimanin shekaru 25 da haifuwa, an shaida cewa ya dade yana yi wa matan unguwar sata, kuma ya saba yin irin haka ga matan aure masu zuwa gaisuwa a unguwa-unguwa bayan Sallar Magariba. Idan ya ga matan suna zuwa sai ya rabe yana jiran isowarsu domin ya samu ya aiwatar da wannan muguwar dabi’ar ta fisgar jaka ya ruga, ya shiga kwana ya tsere musu.
Kamar yadda ya saba yi wa mata, a ranar sai ya gwada kwarewarsa a kan jakar wani bako dan kasuwa mai suna Adamu Achida, inda ya lababo ya samu ya sungume jakarsa da ya ajiye a kofar daki, inda aka sauke shi ya tafi zai yi dahara.
Daidai lokacin da barawon zai wuce da jakar, sai wani dan banga da ke kusa ya daka masa tsawa, inda ya gudu amma ya samu damar kamo shi.
Shugaban ’yan bangar Jihar Edo, Alhaji Shu’aibu Muhammad KT ya shaida wa Aminiya cewa barawon yana a hannunsu suna yi masa tambayoyi kuma yana ba da hadin kai. Ya ce a shirye suke su mika shi ga hukumar ’yan sanda da zarar sun kammala bincikensu.