‘Barawon kayan lantarki’ ya mutu a cikin taransufoma a Zariya

Sai dai har yanzu ba a san daga inda matashin ya fito ba

‘Barawon kayan lantarki’ ya mutu a cikin taransufoma a Zariya

Wutar lantarki Najeriya

Wani mutum da ake zargin mai sace kayan na’urar rarraba hasken lantarki (taransufoma) ne ya mutu lokacin da ya shiga cikin na’urar a unguwar Wusasa da ke Zariyan Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce na’urar dai ita ce take ba Unguwar Kuregu da ke Wusasan wutar lantarki, kuma ya mutu ne yana kokarin yin sata a ciki.

Matashin dai ya gamu da ajalinsa ne da misalin karfe 4:00 na safiyar Lahadin da ta gabata, in ji mazauna yankin.

A cewarsu, sun sanar da Mai Unguwa abin da suka gani kafin daga bisani aka sanar da ofishin yanki na Rundunar ’Yan Sanda da ke Dan Magaji, a Zariya.

Jami’an ’yan sandan dai daga bisani sun dauki gawar matashin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya domin ajiya.

Sarkin Wusasa, Injiniya Isiyaku ya tabbatar wa da wakilinmu cewa ko a makon da ya gabatasai da barayin suka sace kayan daya daga cikin na’urorin unnguwar.

Ya ce wannan karon Allah ne ya kama musu shi, sai dai suna zaton abokan satar nasa sun tsere. Ya ce har yanzu ba su iya gane daga inda mutumin ya fito ba ko wanda ya san shi.