Barawon mota ya kira wa kansa ’yan sanda bayan ta kulle shi

A lokacin da ake ta bikin Kirsimeti ne da sanyin safiya, wani barawon mota ya shiga cikin wata mota da yake son sacewa, sai bai yi sa’a ba, bayan da motar ta kulle shi, lamarin da ya sa tilas ya kira wa kansa ’yan sanda a birnin Trondheim na kasar Norway don neman agaji. Manajan […]

Barawon mota ya kira wa kansa ’yan sanda bayan ta kulle shi
Barawon mota ya kira wa kansa ’yan sanda bayan ta kulle shi

A lokacin da ake ta bikin Kirsimeti ne da sanyin safiya, wani barawon mota ya shiga cikin wata mota da yake son sacewa, sai bai yi sa’a ba, bayan da motar ta kulle shi, lamarin da ya sa tilas ya kira wa kansa ’yan sanda a birnin Trondheim na kasar Norway don neman agaji.

Manajan ’yan sandan Trondelag mai suna Ebbe Kimo a Norway ta Tsakiya, ya ce, barawon motar ya kira ’yan sandan  ne da misalin karfe 8:00 na safe lokacin yana cikin motar da ya bude ya shiga, kamar  yadda kafar labaran jihar ta NRK ta sanar.

A lokacin da yake cikin motar ya yi yunkurin bude motar amma motar ta ki budewa, barawon dai ya san yadda jami’an tsaron suke gudanar da ayyukansu, don haka ya yanke shawarar kawai ya kira su domin neman agaji. Ya dai kira jami’an tsaron ne kamar yana kiran abokinsa da nufin taimaka masa ficewa daga cikin motar.

Ebbe ya ce, barawon dan shekara 17 ya yi yunkurin bude motar kirar Bolbo wacce aka ajiye daga wajen sayar da motoci na daya daga cikin biranen kasar Norway, wajen da aka ajiye motar yana kusa gidan yari. Barawon dai ya bude motar ce ba tare da ya lalata ta ba, kuma da shigarsa ciki kawai sai na’urorin rufe motar suka kukkulle kofofinta.

’Yan sandan sun ce, sun samu barawon a cikin motar yana cikin damuwa, “Amma a lokacin da muka zo yi masa agaji sai hankalinsa ya kwanta,” Kamar yadda suka bayyana wa kafar labarai ta TB2

Ebbe ya kara da cewa, “Jami’anmu na sane da irin laifuffukan da matasan yankin ke aikatawa, ciki har da satar motoci, sai dai wannan barawo  ba ya cikin wadanda suka shahara a satar mota, a satar motarsa ta farko ya yi nasarar fita daga cikin motar da ya yi yunkurin sacewa.”

Ebbe ya bayyana wa, jaridar BG cewa ’yan sanda na kokarin dakile laifuffuka sosai a yankin, duk matasan da aka kama da laifi sai an tuhume su kafin a sake shi zuwa gida, kuma abu ne mai kyau duk inda mutum ya samu kansa cikin kunci ya kira ’yan sanda don neman agaji.

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo