barawon waya ya yanka wata mace a Zariya

Wani da ake zargin barawon waya ne ya yanka wata mace a Zariya, inda kuma ya tsere bayan yin wannan aika-aika.Wakilimu wanda ya ziyarci Unguwar kofar Kuyambana da ke birnin Zariya a Jihar Kaduna domin jin yadda aka wayi gari da jimamin yanka matar mai suna A’isha da aka fi sani da ’Yar Chalaran mai […]

barawon waya ya yanka wata mace a Zariya

Wani da ake zargin barawon waya ne ya yanka wata mace a Zariya, inda kuma ya tsere bayan yin wannan aika-aika.
Wakilimu wanda ya ziyarci Unguwar kofar Kuyambana da ke birnin Zariya a Jihar Kaduna domin jin yadda aka wayi gari da jimamin yanka matar mai suna A’isha da aka fi sani da ’Yar Chalaran mai kimanin shekara 35, an shaida masa cewa an kashe ta ne a gidansu Mai lamba 65 da ke kofar Kuyambana.
Yanka A’isha ya jefa mutanen cikin rudani da mamaki, inda aka samu mabambatan bayanai a kan kisan nata.
Mahaifiyar marigayiyar mai suna Malama Rabi ta shaida wa Aminiya cewa: “Allah Ya jarrabe ni da rashin lafiya sai ’yata A’isha ta zo yi min jinya, kuma tana kula da ni sosai. To a ranar Laraba da daddare da misalin karfe 2:00 na dare sai na ji ana turo mana kofa, na ce wa ke turo mana kofa cikin daren nan sai na ji an yi shiru. Na kasa barci na kuma kasa daurewa duk da ba ni da lafiya sai da na fito amma ban ga kowa ba. Bayan na koma na kwanta sai aka sake dawowa aka shigo dakin da muke kwance tare da marigayiyar, ashe wanda ya shigon har ya ketara inda marigayiyar take kwance ya dauke waya daya, a lokacin ko me yake nufin yi Allah Ya bar wa kanSa sani, can ina jin motsi sai ihu, ita kuma ’ya ta Aisha tana farkawa ko ta riko shi ne kawai sai ya burma mata wuka a gindin kunne a inda ya farke jijiyar wuyanta,” inji ta.
Ta kara da cewa, “Sai na yi wuf na kama shi, to ba ni da lafiya sai ya banke ni ya fita a guje, ina ta ihu kafin mutane su kawo mana dauki, aka dauki marigayiya Aisha aka kai asibiti, kafin gari ya waye ta rasu.”
Malama Rabi ta ce a zatonta ba barawo ba ne, akwai abin da ya kawo shi, domin A’isha daban take a cikin ’ya’yanta saboda irin yadda take hulda da jama’a. Kuma kasancewarta mai haba-haba da jama’a da tausayin al’umma, tana zaton ko wani ne yake jin haushinta ya zo ya kashe ta.
Malama Rabi ta ce ta yi babban rashi domin ko ’ya’yan marigayiyar ba za su kai ta damuwa ba saboda yadda take kula da ita.
Wani dattijo mai suna Abdulmumini wanda aka fi sani da Abdun Baba ya bayyana wa Aminiya cewa duk da ba a san wanda ya aikata wannan mummunan al’amari ba, amma suna zargin barawo ne, kuma sun dukufa wajen rokon Allah Ya tona asirin wanda duk ya aikata haka ga wannan baiwar Allah. Rundunar ’yan sandan yankin Zariya ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta dukufa wajen bincikowa tare da kama duk wanda ya aikata hakan kuma tuni suka tura wa sashin bincike mai zurfi da ke hedikwatarsu a Kaduna batun.