barayi ke haddasa galibin rikicin jihohin Bauchi da Kaduna da Filato – Shehu Aljan
Wani fitaccen mai kama ’yan fashi da makami daga Jihar Bauchi Alhaji Shehu Musa Aljan ya ce galibin rikicin da ake yi a jihohin Bauchi da Kaduna da Filato barayin shanu da ’yan fashi ke haddasawa.Alhaji Shehu Aljan ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da wasu mutum 12 da ake zargi da fashin […]

Wani fitaccen mai kama ’yan fashi da makami daga Jihar Bauchi Alhaji Shehu Musa Aljan ya ce galibin rikicin da ake yi a jihohin Bauchi da Kaduna da Filato barayin shanu da ’yan fashi ke haddasawa.
Alhaji Shehu Aljan ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da wasu mutum 12 da ake zargi da fashin shanu da sauran miyagun ayyuka da suka addabi jihohin Bauchi da Filato kafin ya mika su ga jami’an tsaro.
Alhaji Shehu Aljan ya mika barayi da ’yan fashin ne tare da shanu 52 da awaki 40 da bindigogi kirar AK47 shida da harsasai da dama da ya kama su da su, inda ya ce daya daga cikin mafasa shanun ya shaida masa cewa akwai shanun da suka sayar Naira dubu 450 da kuma wasu dabbobi da suka sayar Naira dubu 80.
Alhaji Shehu Aljan ya ce ya kama wadanda ake zargin ne a garuruwan boto da Mangu da ke jihohin Bauchi da Filato da kwasu wurare, inda ya ce, “Yawanci rigingimun da ake yi a jihohin Bauchi da Kaduna da Filato wasu marasa kaunar zaman lafiya ke haddasa su don sace dukiyar jama’a da kuma haifar da fadan kabilanci da na addini,” inji shi.
Ya roki al’ummomin jihohin da ake samun rikici a yankunansu su ji tsoron Allah su samar da zaman lafiya, kuma su fahimci cewa wannan kasa tasu ce gaba daya ba mai korar wani.
Sai ya yaba wa Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Alhaji Mohammed D. Abubakar kan farfado da aikin tantance ’yan sanda, inda ya ce hakan zai dawo da martabar aikin a kuma magance matsalar tsaro da ke addabar jama’a. Ya ce akwai mutanen da ba su dace da aikin dan sanda ba amma suna ciki kuma suna hana ruwa gudu saboda cin hanci da rashawa. “Mukan fuskanci matsala sosai daga wasu ’yan sanda da idan muka kama wadanda ake zargi da laifi muka mika musu da cikakkun shaidu sai su sake su, su dawo suna yi mana barazana. Misali a Jihar Filato na kama wasu da shanun sata da makamansu, amma sai aka juya maganar aka kama ni aka tsare, sai da aka yi bincike aka gano gaskiyata aka sake ni,” inji shi.
Ya ce a Jihar Kaduna ma ya taba kama mutane ya mika ga ’yan sanda amma aka sake su, kuma aka dawo aka sake tsare shi aka kamo su aka hada shi da masu laifin aka tura Abuja daga baya aka sake shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi Haruna Mohammed ya yaba kokarin Shehu Aljan na taimaka musu wajen farauto masu aikata laifi.