Barayi sun addabi talakawa a Kano
Daga bara zuwa bana talakawan Jihar Kano suna fama da barayi ko ma a ce manyan ’yan fashi da ke bi gida-gida, don kwace wa mutane wayoyin hannu da kayan adon mata masu sada na zinariya. A wasu lokutan idan barayin suka duba suka ga babu kudi, to sukan cutar da al’umma, har ma idan […]
Daga bara zuwa bana talakawan Jihar Kano suna fama da barayi ko ma a ce manyan ’yan fashi da ke bi gida-gida, don kwace wa mutane wayoyin hannu da kayan adon mata masu sada na zinariya. A wasu lokutan idan barayin suka duba suka ga babu kudi, to sukan cutar da al’umma, har ma idan ba a yi sa’a ba sai a ji sun harbi wanda tsautsayi ya auka a kansa. Mutanen da zaune a unguwannin Gwammaja da Kwacirin Jobe da Kurna Rijiyar Lemo, su ne manyan shaidu kan abin da ke faruwa, tunda a daukacin wadannan unuwanni an yi bakin dare sanye kanyan soja da na ’yan sanda. Ko me Gwamnatin Jihar Kano ke yi don bai wa al’umma kariya daga miyagun mutane?
Babban abin takaici a irin wannan artabu da ake yi tsakanin talakawa da barayi, sai ka ga babu wani jami’in tsaro da ke kawo dauki. Kuma koda an bayar da labarin abin da ya auku ga jama’a, babu wasu jami’an gwamnati da za su zo unguwar don jajanta wa al’umma, su kuma tattara bayanai ta yadda za samu karin haske wajen tunkarar masu aikata irin wannan miyagun laifuka.
Duk da cewa Gwamnatin Jihar Kano ita ce mai babban laifi wajen nuna gazawa, da kasa bai wa al’umma kariya, wajibi ne mu zargi kawunanmu, tunda ba ma gudanar da tarurrukan tsauro a unguwanmi, ba mu nemi kulla alaka da jami’an tsaro ba, ta yadda za a raba lambobin neman agajin gaggawa idan musifar barayi da ’yan fashi ta tunkaro mu. Sannan a cikin al’umma a kwai miyagu wadanda za a iya amfani da su, don su bayar da bayani ga ’yan fashi kan wani mutum mai dukiya a unguwa.
Tunda Kano garin addini ne, ya kamata mutane su sani, kada wani mutumin da ba a sani ba, ya shigo unguwa ya kama hayar gida, a ba shi ba tare da an san sana’arsa ba; an tantance matar da suke tare, matarsa c eta aure. Domin a cikin Alkimiyyatus Sa’ada na Imamu Al-Ghazali, ya ce, “ku bayyana aure da wutar girki da kida,” wato ku yi nuni da abin da zai akfa wa al’umma hujja cewa wadannan mutane ma’aurata ne da suka hadu bisa tsarin shari’a don gina iyali; wannan hujja ta Al-Ghazzali ba dama ba ce ga mutane su shantake wajen bidi’o’i marasa kan gado a loakcin bikin aure. Manufa dai mu abbatar da abin da zai bai wa al’ummar kariyar tsaron dukiya da rayuwa, ya kuma kare nasabar iyali.
A hakikanin gaskiya kusan kowane babban layi a sabon garin Kano ana ba shi kariyar tsaro, inda jami’an ’yan sanda ke yin dako a mashigin layin, to me yasa ba za a aiwatar da irin wannan tsarin tsaro a unuwannin rimin kebe da Birget da Kurna Rijiyar Lemo da sauran unguwannin talakawa? Lallai wannan abin dubawa ne. Kuma kowa ya san a cikin sabon garin Kano a kwai wuraren masha’a, amma ana ba su kariya ta musamman, to me ya sa ba za a bai wa talaka kariya a makwancinsa ba?
Jami’an tsaro a ji tsoron Allah, a daina bayar da hayar kayan aiki ko tufafin kayan sarki haya ga bata gari. Ku fadakar da al’umma hanyoyin da ya akmata su bi wajen taimaka wa harkar tsaro a kasar nan. Gwamnatin Kano ki bayar da tsaro a unuwannin talakawa. Ku kuma talakawa ku taima wa kawunanku, wajen kyautata zamantakewa a tsakaninku, tare da bin doka da oda.
A leka kowace mafaka ta miyagu, tun daga kwanar dan gora zuwa cikin garin Kano. Domin idan mutum ya baro Zariya da daddare akwai wasu barayi da ke yi wa al’umma fashi. Kuma jami’an ’yan sanda da kansu sun tabbatar Fulani ne da wasu gungun batagari. To Miyetti Allah aiki ya sameki. Ki zakulo wadannan Fulani, don kada su bata mana suna. Idan kuma ba Fulani ba ne, to wajibi ne miyetti Allah ta yi kokarin wanke su. Saboda a hakiknain gaskiya fashin da ake yi tundaga Katari ta Jihar Kaduna zuwa Dakatsalle ko Kwanar dangora, ana zargin Fulani.
Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, wajen nusar da gwamnatin jihar Kano, kai har ma da ta tarayya da ta kara kaimi wajen kula da harkokin tsaro. Mu kuwa daukacin talakawa wajibi ne idan muka ga wani mutum da ba a gane masa ba, to mu kai rahotonsa ga hukuma. Kuma hakki ya rataya a kan kowa, duk wanda ya ga wata mafakar miyagu ya kai rahoto, inda ya dace. Mu kara kokarin wajen tarbiyyar iyali, ta hanyar nuna wa kananan yara kyawawan dabi’u, kuma su guji cutar da al’umma, don akwai sakamakon Allah a gidan duniya da lahira. A ci gaba da gudanar da addu’o’in neman agajin Allah, don karya lagon miyagu: ‘yan fashi da makami da masu fashi da mukami. Allah Ya ba mu kariyarSa daga abin da miyagun mutane da shaidanu ke aikatawa, a cikin duhun dare, safiya da marece.
Sharhabillu Ibrahim Jabbi ya rubuto makalarsa daga Kwachirin Jobe a Kano.