barayi sun bindige dillalin shanu a Benin

Wasu gungun mutane wadanda ake kyautata zaton  barayi ne wadanda ba a san daga inda suka fito ba, suka tare wani dillalin shanu, mai suna Muhammadu Inuwa, wanda aka fi sani da suna Alhaji Baba Fajewa Suka bindigeshi, bayan da ya harkokinsa a kasuwa yana tafiya gida, a yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, […]

barayi sun bindige dillalin shanu a Benin
barayi sun bindige dillalin shanu a Benin

Wasu gungun mutane wadanda ake kyautata zaton  barayi ne wadanda ba a san daga inda suka fito ba, suka tare wani dillalin shanu, mai suna Muhammadu Inuwa, wanda aka fi sani da suna Alhaji Baba Fajewa Suka bindigeshi, bayan da ya harkokinsa a kasuwa yana tafiya gida, a yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, da misalin karfe  8:30 na dare, a kusa da gidan a Unguwar Eyaen da Urora da aka fi sani da Old Road kan iyakar karamar Hukumar Uhonmwode da ke Jihar Edo.
Muhammadu Inuwa, wanda aka fi sani da Alhaji Baba dan asalin garin Fajewa ne nta karamar Hukumar Takai a Jihar Kano. An kashe shi yana mai kimanin shekaru 52 a duniya, kuma yana da matan aure su biyu, tare da diya mace guda daya tilo, wadda take gidan mijinta. Ya kuma bar mahaifiyarsa da ‘yan uwansa su hudu, a ciki akwai mai suna Sulaimanu Inuwa Fajewa.  
Sulaimanu dai kani ne ga marigayin, wanbda ya bayyana cewa: ‘’Marigayi ddan  uwana Alhaji Baba, mutum ne mai kulawa da addini, kuma mai tattali ba yia danuna kwadayi ga kayan mutane, kuma yana son zaman lafiya a duk harkokinsa mutumne mai taimakwa iyaye da sauran yan uwa saboda haka babu abinda muka iya yi sai dai addu’a Allah ya jikanshi inji kaninsa sulaimanu.
Amininsa Malam Auwalu Burum Burum yace ‘’A lokacin da za mu tafi gida marigayin ya kira ni a waya cewa in zo mu tafi, sai na tashi na je na same shi a wurin wani mai shayi, sai muka hadu muna tafiya, muna hira har muka yi kusa da gida, sai muka gani wasu mutane suka gitta mana a gabanmu, dauke da makami suka fara yi mana magana da harshen, cewa ku kawo kudi (bring money). Kafin kace kwabo dayan daga cikinsu sai ya daga bindiga ya harbi marigayin a goshi a take ya fadi ya mutu. Sai suka zo kansa suka caje shi, suka debi abin da ke cikin aljifansa. Daga nan sai suka juya akaina, suka kama cajina suka debe komai, suka barni haka, suka juya suka kama hanya suka tafi. Daga nan sai  na tashi na je akan marigayin na daga shi ina? ya rigamu gidan gaskiya.”
Musta Jamis jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yansan shiyyar Eyaen, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce suna akan bincike, tare da neman wadannan miyagun mutane da suka aikata wannan kisar gillar.
 ‘’A yanzu haka mun sa ma’aikatamu sun dukufa wajen neman wadannan mutanen, kuma ina ganin za su shiga hannu cikin kankanin lokaci. A duk inda suke cikin wannan jihar, don haka hukumar mu ta ‘yan sanda tana kira ga jama’a su ba mu goyon baya da bayanan sirri na gaskiya game da irin wadannan miyagun,”  inji shi.