barayi sun dawoda mota kwana daya bayan sace ta

A makon jiya ne aka gano wata mota da wasu barayi suka sace a Jihar Indiana ta kasar Amurka, bayan da suka aike wa mai motar mukullansa da kuma takardar neman gafara kwana daya bayan sace ta, kamar yadda shafin Intanet na fod 59.com ya wallafa. Kyle Moeller, wanda shi ne mai motar, ya ce […]

barayi sun dawoda mota kwana daya bayan sace ta
barayi sun dawoda mota kwana daya bayan sace ta

A makon jiya ne aka gano wata mota da wasu barayi suka sace a Jihar Indiana ta kasar Amurka, bayan da suka aike wa mai motar mukullansa da kuma takardar neman gafara kwana daya bayan sace ta, kamar yadda shafin Intanet na fod 59.com ya wallafa.

Kyle Moeller, wanda shi ne mai motar, ya ce cikin takardar da suka aike masa ta akwatin Gidan Waya sun yi bayanin wurin da za a je a samu motar. Bayan sanar da ’yan sanda abin da ke faruwa ne, sai suka yi amfani da bayanin da ke kunshe cikin takardar, inda suka same ta kasa da nisan mil daya daga gidan da barayin suka saceta.
Mista Kyle ya ce ya yi farin ciki matuka da gano motar, kuma ya ce “tun da nake ban taba jin wurin da aka sace mota aka dawo da ita ba.”
Binciken ’yan sanda ya nuna cewa fahimtar da barayin suka yi cewa za su shiga hannu shi ne babban dalilin da ya sa suka dawo da motar. Kodayake, rundunar ’yan sanda jihar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike don gano barayin.