barayi sun fada gidan shugaban ’yan Arewa a Benin
A makon da ya gabata ne wani gungun matasa da ake kyautata zaton na ’yan fashi ne dauke da makamai suka yi wa gidan shugaban al’ummar Arewa mazauna Benin, Alhaji Badamasi Saleh dirar mikiya, inda suka fara da harbe-harbe na tsoratarwa a cikin gidansa. Miyagun sun shigo unguwar da shugaban yake da zama, wato Lagos […]
A makon da ya gabata ne wani gungun matasa da ake kyautata zaton na ’yan fashi ne dauke da makamai suka yi wa gidan shugaban al’ummar Arewa mazauna Benin, Alhaji Badamasi Saleh dirar mikiya, inda suka fara da harbe-harbe na tsoratarwa a cikin gidansa.
Miyagun sun shigo unguwar da shugaban yake da zama, wato Lagos Street, cikin garin Benin, kamar yadda wadanda suka shaida. Sun ce al’amarin sun ce miyagun sun yi badda kama, fuskokinsu duk a lullube kuma suna dauke da makamai irin na gargajiya da na zamani.
A cikin bayaninsa da ya yi wa Aminiya, Shugaba Badamasi ya ce wadannan miyagun sun zo masa a ba-zata a gidansa. “Miyagun ta bayan gida suka hau katanga suka dira cikin gidana, sai dai a lokacin ba na cikin gidan, na fita na je shago domin sayae kati. Ina dawowa ke nan sai na ji harbin bindiga a cikin gidana, abin ya ba ni mamaki matuka. Na yi sauri na shiga gida, domin tunanin irin abin da barayin suke yi na keta haddi ga matan aure.”
Ya kara da cewa, lokacin da ya shiga cikin gidan sai ya tarar da mutum biyu sun shiga dakin makwabcinsa, suka daga bindiga suka yi harbi amma kuma wannan bai razana su ba. “Da suka ga haka sai suka fita a guje za su je su tarar da ’yan uwansu da ke boyen, sai muka yi kukan kura muka bi su, muka kama su; sauran suka arce,” inji shi.
Ya ce harbe-harben kan mai uwa da wabin da barayin suka yi bai kai su ga biyan bukata ba, domin tare da taimakon Allah jama’a ’yan unguwa da ’yan sanda sun samu an cafke wasu daga cikin ’yan fashin mutum biyu, wato Ibrahim Buba da Nasiru Jibrila, wadanda ya zuwa rubuta rahoton nan suna hannun hukumar ’yan sanda na Jihar Edo.