Barayi sun haka riyojin mai a gidajensu
Hukumar NDLEA a Jihar Legas ta kama wasu magidanta kan zargin haka rijiya don satar man fetur a unguwar Ejibo da ke jihar.Aminiya ta gano cewa wadanda ake zargin sun haka rijiyar ta yi zurfi daidai inda bututun kamfanin mai na NNPC ya ratsa ta cikin gidajensu suka fasa bututun suna kwasar mai suna sayarwa […]

Hukumar NDLEA a Jihar Legas ta kama wasu magidanta kan zargin haka rijiya don satar man fetur a unguwar Ejibo da ke jihar.
Aminiya ta gano cewa wadanda ake zargin sun haka rijiyar ta yi zurfi daidai inda bututun kamfanin mai na NNPC ya ratsa ta cikin gidajensu suka fasa bututun suna kwasar mai suna sayarwa ba bisa ka’ida ba.
Gidajen da lamarin ya shafa sun hada da gida mai lamba 17 da mai lamba 30 da ke unguwar Ejigbo amma tuni jami’an hukumar NDSC da na soja suka killace wurin.
Sai dai wadanda ake zargi sun musanta zargin da ake yi musu inda daya daga cikinsu mai suna Misis Funke Ogunba wacce ta shafe shekara takwas a gidan ta ce kwanan nan suka gano cewa mai yana malala a rijiyarsu.
Ta ce, “Shekaru da dama muna dibar ruwa a rijiyarmu, sai a watan jiya muka gano mai yana malala a cikin rijiyar, nan da nan maigidana ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na unguwar Ejigbo da kuma jami’an kamfanin NNPC. Sun zo nan har sau biyu suka gaya mana cewa ranar Litinin za su zo su duba idan mai ya ci gaba da malala za su toshe rijiyar su haka mana wata.”
Shi ma Mista Aromasogo mai kimanin shekara 60 da aka kama tare da matarsa da ’ya’yansa a gidansa mai lamba 17, ya yi ikirarin sayen gidan a wurin wani mutum tare da rijiyar ba tare da sanin mai yana malala a cikinta ba.
Ya ce “Sai daga baya na gano mai yana malala a rijiyar, kuma nan da nan na sanar da ’yan sanda da jami’an kamfanin NNPC inda suka yi mana alkawarin za su toshe rijiyar.”
Amma Kwamandan Hukumar NSCDC Mista Adesuyi Dayo ya ce bayanan da mutanen suka bayar zuki-ta-malle ne kawai domin bincikensu ne ya gano masu gidajen sun haka rijiyoyin ne suna satarsa.
Kwamandan Rundunar Soja ta Tara Birgediya Adeniyi Oyebade ya ce sojoji za su ci gaba da goya wa Hukumar NSCDC baya don maganin batagari.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin babban jami’in ofishin ’yan sanda na Ejigbo ya ki cewa uffan, ya ce sai dai a tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar.
Kakakin Misis Ngozi Braide ta ce ba za ta iya cewa komai ba domin lamarin yana hunnun Hukumar NSCDC.