barayi sun halaka masu gadi uku
Wasu gungun mutane wadanda ba a san daga inda suka fito ba, sai dai ana kyautata zaton ’yan fashi suka abka wa wani wuri, inda ake sayar da motoci a Unguwar Eyaen, daura da babban titi da ta fito daga cikin garin Benin zuwa Auchi; daren yammacin Litinin da ta gabata da misalin karfe 12:30 […]
Wasu gungun mutane wadanda ba a san daga inda suka fito ba, sai dai ana kyautata zaton ’yan fashi suka abka wa wani wuri, inda ake sayar da motoci a Unguwar Eyaen, daura da babban titi da ta fito daga cikin garin Benin zuwa Auchi; daren yammacin Litinin da ta gabata da misalin karfe 12:30 na daren.
Wadannan miyagun kamar yadda shaidun gani da ido na unguwar suka bayyana wa Aminiya, bayan faruwar lamarin sun ce cikin dare da misalin karfe 12:30 suka fara jin wata hayaniya tana tashi, a inda ake sayar da motoci na wannan wurin.
“Wata hayani muka fara ji daga wurin wannan yadin, inda aka tara motocin sayarwa. Ashe ba mu sani ba, miyagun mutane ne suka shiga wurin, suka tarar da masu gadin wurin, sai suka hau su da sara da adduna. Suka kashe guda uku, suka raunata wasu guda biyu, wadanda a yanzu haka an kai su wani asibitn cikin garin Benin domin jinya.” Inji shaidun.
Wadanda barayin suka kashe din su ne Babangida Ibrahim da Haruna Audu da Muhammad A. Audu. Wadanda suka samu raunuka kuma suke kwance a asibiti sun hada da Ya’u Muhammad da Isah Abubakar wanda aka fi sani da Baballi. Dukkansu sun fito ne daga karamar Huku=mar Nangere a can Jihar Yobe.
’Yan uwan wadanda miyagun suka kashe, Dauda Abdullahi, Yunsa Muhammed da Malam Adamu Abdullahi sun nuna alhininsu a kan rasuwar ’yan uwansu tare da tausaya wa wadanda suke kwance a asibiti. “Miyagun mutane marasa imani, sun yi wa ’yan uwanmu kisan gilla, kisan walakanci. Mun bar su da Allah, ba mu da abin da za mu ce, babu abin da za mu iya a kai, sai dai mu yi wa wadannan ’yan uwanmu da suka riga mu gidan gaskiya kyakkyawar addu’a Allah jikansu da rahamarSa.” Inji Malam Adamu.
Sai dai ya zuwa hada rahoton nan, hukumar ’yan sandan jihar ba ta ce komai ba a kan faruwar lamarin; domin duk kokarin Aminiya don samun karin haske daga bangaren hukumar ba a samu biyan bukata ba. Saboda a lokacin da wakilinmu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a, DSP Osifo A. ya ce babu wani rahoto da ya iso gare su mai kama da hakan. Amma kuma wani jami’in na ’yan sanda, wanda bai so a fadi sunansa ba, ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin amma shi ma bai dora wani karin bayani ba.