Barayi sun kashe mutum 22 a Zamfara

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe akalla mutum 22 a kauyen Malikawa da ke lardin Gidan Goga a karamar hukumar  Maradun ta jihar Zamfara. Yankin Gidan Goga ya dade yana fama da hare-haren wasu ‘yan bindiga da ke amfani da babura a kwanakin baya. ‘Yan fashi da makami da barayin […]

Barayi sun kashe mutum 22 a Zamfara

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe akalla mutum 22 a kauyen Malikawa da ke lardin Gidan Goga a karamar hukumar  Maradun ta jihar Zamfara.

Yankin Gidan Goga ya dade yana fama da hare-haren wasu ‘yan bindiga da ke amfani da babura a kwanakin baya.

‘Yan fashi da makami da barayin shanu sun kashe mutum 60 a kauyuku bakwai duk a yankunan lardin daga watan Mayu zuwa Yuli na shekarar 2018.