barayi sun kona motar Yakubu M. Kumo
A ranar Lahadin da ta gabata ne barayi suka kona motar fitaccen marubucin labaran fina-finan Hausa Yakubu M. Kumo kirar Hennesy 2000 a wani hotel da ke garin Dutse a Jihar Jigawa bayan sun yi yunkurin sace motar sun gagara saboda na’urar tsaro da aka sanya mata.Kumo ya ce al’amarin ya faru ne da misalin […]

A ranar Lahadin da ta gabata ne barayi suka kona motar fitaccen marubucin labaran fina-finan Hausa Yakubu M. Kumo kirar Hennesy 2000 a wani hotel da ke garin Dutse a Jihar Jigawa bayan sun yi yunkurin sace motar sun gagara saboda na’urar tsaro da aka sanya mata.
Kumo ya ce al’amarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na dare, bayan sun dawo daga daukar fim dinsa mai suna ‘Asibitin kauye’. “Bayan mun dawo daga kauyen da muke daukar fim din sai muka samu motoci sun cika harabar hotel din. Motata ce ta karshe a cikin jerin motocin da suka shigo hotel din, sannan ita ce ba ta samu damar shiga otel din ba, hakan ya sanya na ajiye motata a waje bayan jami’an hotel din sun ba ni tabbacin babu abin da zai faru, sun ce mini idan motoci suka cika wurin da aka tanada don ajiye motoci da ke hotel din akan ajiye su a waje.” Inji shi.
Ya ce: “Muna kwance cikin dare sai muka ji ana buga mana kofa ana ihun wuta! Wuta!! Muka farka a razane. Bayan mun fito ne sai muka ga mota tana cin wuta daga baya aka gane tawa ce.”
Da Wakilinmu ya tambaye shi me ake zargin ya yi sanadiyyar tashin wutar sai ya ce: “Zargi mafi girma dai shi ne, barayi ne, domin akwai wadanda suke makwabtaka da hotel din sun ce, motar ta dade tana kara kusan minti 30, alamar ana so a sace ta ne. Daga baya sai suka ji shiru, inda kuma daga baya suka tarar da motar tana ci da wuta. Da ma na sanya wa motar tawa na’urar tsaro da za ta hana ta tashi ko da an bude ta.”
Da aka tambaye shi kasancewar motarsa ba ta samu shiga ba shin jami’an hotel din ba su ajiye wanda zai lura da ita ba? Sai ya ce, ai hotel din karami ne, ba su da manyan jami’an da ke lura da hotel din. Mutum daya ne a lokacin wato mai karbar baki shi ma kuma ya yi barci lokacin da al’amarin ya faru.
A karshe ya ce, ba zai dauki wani mataki ba duk da cewa masu aiki a hotel din sun ba shi tabbacin babu abin da zai faru, ya dauki hakan a matsayin kaddara ce daga Allah.
A yanzu an kammala daukar fim din, kowa ya koma gida.