Barayi sun sace buhun shinkafa a gidan mataimakin firinsifal
Bata-gari sun haura gidan mataimakin firinsifal sun sace buhun shinkafa
Barayi sun haura gidan wani Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandaren Abaji da ke Abuja sun yi awon gaba da buhun shinkafarsa tare da keken dinki guda daya.
Mataimakin Shugaban Makarantar ya ce a ranar Juma’a wasu bata-gari suka shiga gidansa da misalin karfe 2:00 na dare suka yi awon gaba da wadannan kayayyaki.
- HOTUNA: Yadda aka naɗa Hadimar Al-Kur’ani Mace ta Farko a Zariya
- Matatar Dangote: Minista na neman sasanta NNPC da Dangote
Ya bayyana cewa ‘yarsa ce ta ankarar da su cewa bata-garin sun tsallako katantagar da dare bayan da ta ji motsinsu a lokacin da ta fito domin shiga bandaki da tsakar dare.
Har wa yau ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka yi wannan aika-aika a unguwar tasu ba, ko mako biyu da suka gabata an haura gidan makwabcinsa an yi irin wannan sata.
Sai dai ko da wakilin Aminiya ya yi yunkurin jin ta bakin ‘yan sanda sun shaida masa cewa a zuwa lokacin ba su da masaniyar wannan lamari.