‘Barayin’ da suka je fashi sun ɓige da satar tukwanen miya da abinci a Kalaba

Sun rika satar abinci da miya, a maimakon kudi ko kayan alatu

‘Barayin’ da suka je fashi sun ɓige da satar tukwanen miya da abinci a Kalaba

Sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka a daren Laraba a Kabala, babban birnin Jihar Kuros Riba, ’yan fashi da makami sun rika bi gida-gida suna sata.

Sai dai sabanin yadda aka saba gani, duk gidan da suka balle suka shiga, a maimakon su ce a ba su kudi da sauran kayan alatu sai su ce abinci da tukwane suke so.

Sukan ce da masu gidan kada su ji tsoro, ba kisa suka zo yi ba ko karbe kudi, a’a tukunyar miyar da abinci suke nema su kwashe kawai.

A unguwannin Mbukpa da Ambo da Adak Uko da ke yankin Karamar Hukumar Kalaba ta kudu, a duk gidajen da suka shiga sukan ce a nuna musu inda aka ajiye miya da abincin gidan.

“Idan maigidan ko.matar gidan suka yi nawar nuna musu wajen da tukwanen suke sai su hau dukan su,” in ji uwargida Affiomg Effiwatt, wata wacce ita ma aka yi wa fashin a Kalaba.

Ta ce tun misalin karfe 2:00 na dare ’yan fashin dauke da adduna da sauran muggan makamai sun rika bi suna fadawa kwararo-kwararo na unguwanmon suna yin aika-aikar.

Affiomg ta kuka ce, “Cikin dare sai na ji ana ta dukan kofar gidana, abu babu misali, har aka balla kofar gidan aka shigo. Da jin haka na ce wadannan barayi ne.

“Sai daya daga cikinsu ya ce ba duka ba zagi, ba mu zo don mu kashe ki ba, ba mu miyar da kika yi, sannan ki hada mana da kudi ki ba mu, abin da muke bukata ke nan,” in ji ta.

Shi kuwa Robinson Elaette, wanda shi ma aka shiga gidan nasa ya ce, “Sun iskeni idona biyu suka kwada min adda a ka, da na tsorata sai suka ce na ba su abincin da muka yi da miya, idan da hali ma a hada musu da kudi.”

Wadanda suka zanta da wakilinmu sun ce sun sanar da hukumar ’yan sanda a ofishinau na Mbakpa, amma kafin su je barayin sun riga sun gama ta’addancim su sun watse Basu kama kowa ba

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Irene Ugbo game da lamarin, inda ta ce, “Da safiyar nan aka sanar wa hedkwatarmu abin da ya faru, amma an dauki matakin dakile afkuwar hakan a nan gaba.”

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7