Barayin da suka sace babura 30 sun shiga hannu

A farkon wannan makon ne asirin wadansu mutum biyar ya tonu lokacin da ’yan sanda suka kama su kan zargin satar sababbin babura kirar Honda fiye da 30 daga Kamfanin Amolad da ke Ibadan. Da yake nuna wa manema labarai babura 22 da aka gano daga hannun wadanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Abiodun […]

Barayin da suka sace babura 30 sun shiga hannu

A farkon wannan makon ne asirin wadansu mutum biyar ya tonu lokacin da ’yan sanda suka kama su kan zargin satar sababbin babura kirar Honda fiye da 30 daga Kamfanin Amolad da ke Ibadan.

Da yake nuna wa manema labarai babura 22 da aka gano daga hannun wadanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Abiodun Odude ya ce, da tsakar dare ne wani mai suna Nurudeen Odetola mai shekara 43 ya jagoranci wadanda ake zargin zuwa ma’ajiyar kaya ta kamfanin da ke daura da Jami’ar Ibadan da  ma’ajiya ta biyu da ke kan hanyar Iwo inda suka daure mai gadi suka balla kofofin suka shiga suka yi awon gaba da baburan.

Kwamishinan wanda ke tare da Mataimakinsa DC Attahiru Isa da manyan jami’an ’yan sanda ya ce bayan samun labarin barnar da aka yi daga shugaban kamfanin, sai ’yan sanda suka fara farautarsu, inda suka yi nasarar kama su duka biyar tare da kwato babur 22. Sai dai mai gadin da suka bar shi a daure ya mutu a dalilin wahalar da ya sha.

Kwamishinan ya kuma nuna wadansu mutum biyar  da aka kama da zargin sace buhunan shinkafa da wasu kaya suka kai na Naira miliyan 10.

Ya ce wadanda ake zargin sun balle kofofin wasu shaguna ne a Unguwar Oke Owode a garin Ogbomoso  suka sace shinkafar suka sayo kananan motoci kirar Gulf guda 5 da Toyota 1.

An same su da manyan guduma da karafunan da suke amfani da su wajen balla kofofin.