barayin dabbobi suna yin illa ga mahauta – Sarkin Fawa

Sabon Sarkin Fawan Katsina Alhaji Usman Sa’idu ya ce barayin dabbobi musamman shanu suna kawo wa sana’ar fawa nakasu a kasar nan.  Sarkin Fawan wanda Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya nada a ranar Asabar da ta gabata ya ce, sun bullo da wasu hanyoyi na dakile waccan muguwar hanyar da batagari […]

barayin dabbobi suna yin illa ga mahauta – Sarkin Fawa
barayin dabbobi suna yin illa ga mahauta – Sarkin Fawa

Sabon Sarkin Fawan Katsina Alhaji Usman Sa’idu ya ce barayin dabbobi musamman shanu suna kawo wa sana’ar fawa nakasu a kasar nan. 

Sarkin Fawan wanda Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya nada a ranar Asabar da ta gabata ya ce, sun bullo da wasu hanyoyi na dakile waccan muguwar hanyar da batagari ke amfani da ita don cutar da al’umma, inda ya ce, “Daga yanzu duk inda wani mahauci za shi sayen dabba a ruga aka gayyace shi ko radin kansa, sai ya sanar da masarautar Sarkin Fawa kafin ya tafi domin sanin irin halin da dabbar da zai sayo take ciki. Haka kuma duk wanda ya kawo dabbarsa mayanka da rai ko a yanke, sai mun san daga inda ya fito tare da kawo mana wani mutun wanda muka sani shi kuma ya san shi.”
Sarkin Fawa Usman ya kara da cewa, wannan kadan ne daga cikin irin hanyoyin da shi da sauran mahauta za su rika bi domin maido da martaba sana’ar a idon jama’a.
Haka zalika, Sarkin Fawan ya ce, batun gyaran wuraren yankan dabbobin da suka fara shiga cikin mawuyacin hali a wasu wuraren na daga cikin ayyukan da zai sa a gaba. “Akwai maganar tsabtace wuri da sanin lafiyar dabba ko naman da za a sayar wa al’umma,” inji shi.
Ya ce, zai yi iya kokarinsa wajen maido da fataken da suka kaurace wa kawo dabbobinsu a mahauta don sayarwa. “Zan yi iya kokarina na bin duk inda na san akwai fataken da a da suke kawo dabbobinsu da suka kaurace, in Allah Ya so nan da dan lokaci sai an ga wuraren da ake ajiye shanu da rakuma sun cika kamar da. Za mu shiga har makwabtanmu don lallaso su, su dawo a ci gaba da harka,” inji shi. Ya ja hankalin mahauta su tsare gaskiya da rikon amana wajen gudanar da sana’arsu.
Sarkin Fawan ya yaba wa Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir a kan irin yadda yake taimakawa ga ci gaban sana’ar da kuma yadda har yanzu bai canza wa sarautar wuri ba.