‘barayin fasaha ke kassara kwazon masu fina-finan Hausa’

A tattaunawarsa da Aminiya, daya daga cikin masu harkar fina-finan Hausa, ta fuskar daukar hoton bidiyo a Legas, Ababakar Ziga, ya bayyana matsalolin da suke ci wa harkar tasu tuwo a kwarya, inda ya bayyana cewa babbar matsalarsu ita ce ta barayin zaune, masu satar fasaha. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Ko za ka gabatar […]

‘barayin fasaha ke kassara kwazon masu fina-finan Hausa’
‘barayin fasaha ke kassara kwazon masu fina-finan Hausa’

A tattaunawarsa da Aminiya, daya daga cikin masu harkar fina-finan Hausa, ta fuskar daukar hoton bidiyo a Legas, Ababakar Ziga, ya bayyana matsalolin da suke ci wa harkar tasu tuwo a kwarya, inda ya bayyana cewa babbar matsalarsu ita ce ta barayin zaune, masu satar fasaha. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ko za ka gabatar da tarihinka a takaice?

Sunana Abubakar Idris kuma an fi sani na da Abubakar Ziga. A garin Garwa da ke kasar Kamaru aka haife ni kuma a can na girma na yi karatu; daga bisani na yo bulaguro zuwa Legas a 2006. A nan na koyi Hausa da Turanci, domin a da ba na jin Hausa sai Faransanci da Fulfulde da wadansu yaruka na can Kamaru.
Ta yaya aka yi ka sami kanka a wannan sana’ar ta daukar hoton bidiyo?
E, to,m bayan na shigo Legas sai na fara ’yan buge-bugena; na dan yi dan fadi-tashi daga bisani sai na yi sha’awar sana’ar daukar hoton bidiyo. Daga nan na rubuta takarda zuwa gidan talbijin na MITb, na bayyana masu sha’awata na koyan sana’ar daukar hoto na bidiyo; suka ce za su koya mini sai dai akwai tsada. Na ce masu babu damuwa, tunda sana’a nake so na koya. Sai suka ce zan biya kudin shekara biyu, domin sai na shafe tsawon wannan lokacin kafin na kware. Nan take na biya Naira dubu 300 da doriya, na tare a can, na fara koyon aiki.
Bayan da na yi wata shida ina koyo, sai na iya sarrafa kyamara. Nan fa suka fada mini cewa in aiki nake so na koya, a yanzu na iya, idan ina so na je na bude sutudiyona ne, to in kuma zan ci gaba da aiki da su ne to sun ba ni zadi. Nace masu a’a, ina bukatar na kara kwarewa, don haka na ci gaba da koyo. Muna kuma fita aiki da neman labarai a waje muna kuma yin aiki a sitidiyo in ya samu. Haka na yi ta yi har tsawon shekara biyu.
Ya aka yi ka fara aiki da masu shirya fina-finan Hausa?
Bayan na yi shekara biyu ina aiki a MITb sai na ga akwai bukatar na sauya wurin aiki, domin a ganina in ba haka na yi ba, ba zan sami mafita ba. Sai na je wajen mai gidanmu, Sulaiman Abubakar na yi masa bayani. Sai ya ce ba damuwa tunda na kware, in zan bude sutudiyona sai na yi, don na sami damar yin aiki a kai-a kai. Daga nan suka buga takardun shaida suka ba ni, suka kuma tambaye ni cewa wace shawara na yanke? Na ce musu a gaskiya ina sha’awar daukar fim. Suka tambaye ni na Hausa ko na Yarabanci ko Turanci? Na ce musu fim din Hausa. Sai suka ce mini za su tura ni Jos amma sai na yi wata uku a can. Na ce masu ba damuwa, nan fa suka rubata takarda na tafi Jos, na iske mutanen da suka karbe ni hannu biyu-biyu. A cikinsu akwai Bello Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Janaral BMB da wani Darakta Auwal. Bayan na huta na kwana uku a otel din da aka sauke ni, sai suka fara fita da ni aiki. Ana haka har suka fara sanya ni a cikin shirin fim. To, haka na fara aiki da kamfanin shirya fina-finan Hausa. Duk loko da sakon da ake shirya fina-finai a Arewa sai da na je na yi aiki. Sai da ya zamo ni da Legas sai dai na zo hutu, na yi mako daya ko biyu, na sake komawa can bakin aikina.
Kasancewarka gwani a sana’ar sarrafa kyamara, ko za ka yi mana karin haske game da saddabarun da kukan yi da ita a yayin daukar fim da ma irin kyamarar da ka fi so ka yi aiki da ita?
E, akwai ’yan dabarun da muke yi da kyamara, sai dai abin sirri ne da ba na so na bayyana ba amma kadan daga ciki shi ne yadda za a shiryar fim ka ga kamar ana ruwa bayan kuwa ba a lokacin damina aka dauki shirin ba; ko ka ga an yi shirin fim da rana kiri-kiri amma an sarrafa kyamark, an mayar da ranar dare ba tare da sai an jira dare ya yi ba; duk da dai wasu daraktocin sun fi son a yi amfani da daren na hakika sai su ba da umurnin a jira daren. Amma duk abin da mutun zai yi ba zai iya mayar da dare rana ba a shirin fim, ita rana dole a jira ta zo tukunna. Kyamarar da na fi so na yi aiki da ita kuwa ita ce Sony, duk da dai tana da tsada amma tana fitar da hoto kwarai, ka ga ya yi tartar kamar yadda ake bukata.
To ko me ya sake dawowa da kai Legas yanzu?
Akwai lokacin da na zo hutu, sai na yi hadari a babur, na karye a kafa; sai da na yi shekara uku ina jinya. Tun bayan nan sun ta bugo mini waya don na koma bakin aiki; bayan sun zo lokuta da dama sun gaishe ni. Sai dai ka ga aikin na bukatar tsayuwa sosai, don sai ka yi aikin awa uku kana tsaye; ka ga haka zai yi wa mai rauni a kafa wuya. To, a yanzu dai da na kara murmurewa ina aiki da ’yan fim din Turanci.
To, ya za ka kwatanta fina-finan Hausa da takwaransa na Turanci, ta bangaren kayan aiki, tunda dai ka yi aiki da dukkaninsu?
A gaskiya a yanzu masu shirya fina-finan Hausa na matukar kokari kuma suna da wadatattun kayan aiki da kwararrun ma’akata, sai dai ba za ka hada su da masu fina-finan Turanci ba a bangaren wadatattun kayan aiki; domin kuwa su sun maida abin sana’a, wacce suka bai wa gaskiya. Sai ka ga mutun guda ya mallaki dukkanin kayan aiki da ake bukata, sai dai kawai a zo a rika dauka haya, ana ba shi kudinsa. Mu kuma masu fina-finan Hausa, mutanen da ke cutarmu su ne barayin fasaha, masu buga jabun fim na dibidi, su ne ke janyo mana asara, suke kassara mana sana’a.
Duba da cewa ka koyi sana’ ar ne a wajen kwararru, ko ya za ka kwatanta irin aikinka da na wadanda suka koya a akasin haka?
Ka ga ni inda na koyi sana’ar, an koya mini ne a ilimance, domin a lokacin muna yin darasu; mu yi rubuce-rubuce da ma daukar jarabawa, ban da kuma uwa-uba gwajin yin amfani da kayan aiki. Ka ga wadanda kan koya da ka babu maganar wannan, sai dai kawai a ce yi kaza ko in ka yi kaza, kaza ne zai faru; wanda ake yi da ka ba tare da bin wani kyakyawan tsari ba.
Wani irin alfanu ko kalubale ka tsinkaya a wannan sana’ar?
Alhamdu lillahi, na amfana kwarai, domin kuwa dawainiyata kaf da ta ’yan uwana da abokan arziki, duk a cikinta nake yi kuma a sana’ar Allah Ya hada ni da abokan hulda na arziki. Duk lokacin da wani lamari ya shige mini duhu sai na kira irin su mai gidana Bello Muhammad Bello, sai ka ga ya ce mini yi abu kaza sannan ka yi haka sai ka ga komai ya yi daidai. kalubalen da na fuskanta kuwa shi ne jinyar da na yi ta tsawon shekara uku, wadda ta dakushe mini harkokina. Duk da haka dai na gode Allah, domin kuwa a yanzu na warke sarai, ina kuma samun ci gaba a sana’ar.