Barayin injinan ban-ruwa da kayan noman RIFAN sun shiga hannu
An cafke mutum biyar kan satar injinan ban-ruwa da kayan noma na N11m, mallakin Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a Jihar Kebbi
Mutum biyar sun shiga hannu kan satar kayan noma na Naira miliyan 11 daga dakin ajiyar Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a Jihar Kebbi.
Asirin barayin kayan noman ya tonu ne a garin Zuru, bayan wani mutum ya kai wa ’yan sanda kara cewa an fasa dakin ajiyar kungiyar RIFAN an sace injinan ban-ruwa da takin zamani da magungunan kashe kwari da na kashe ciyawa da kuma famfunan feshi.
- Matar da ke kai wa ’yan bindiga abinci ta shiga hannu a Kwara
- NAJERIYA A YAU: Me Ke Sa Tinubu Baya-baya Da Shiga Jama’a?
Kakakin ’yan sanda na Jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya ce a lokacin da suke bincike sun gano tare da cafke wani wanda ya taya barayin jigilar kayan satar, “wanda bayan an yi masa tambayoyi ya fallasa wasu mutum hudu.
“Sauran wadanda ake zargin duk sun shiga hannu kuma sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.”
Jami’in ya ce a yayin bincike, an gano cewa duk kayan da aka sace din suna hannun daya daga cikin mutanen.
Ya ce kawo yanzu an kwato injinan ban-ruwa guda tara da kuma kwali 45 na maganin kashe ciyayi a hannunsu.