Barayin mota sun shiga hannu a Kebbi

‘Yan Sanda a Jihar Kebbi sun yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota, wadanda kuma suke addabar al’umma da sace-sace a jihar. Bayanin haka ya fito ne daga bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi, CP Ibrahim M. Kabiru yayin da ya ke yi wa manema labarai karin haske a […]

Barayin mota sun shiga hannu a Kebbi
Barayin mota sun shiga hannu a Kebbi

‘Yan Sanda a Jihar Kebbi sun yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota, wadanda kuma suke addabar al’umma da sace-sace a jihar.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi, CP Ibrahim M. Kabiru yayin da ya ke yi wa manema labarai karin haske a ofishinsa da ke Birnin-Kebbi.

Kwamishinan ya ce jami’ansa sun fantsama ne fagen neman barayin motoci da suka addabi jama’ar Jihar Kebbi, saboda irin yawan koke-koke da muke ta samu kan sace motoci a jihar”. Inda kuma jami’an rundunar ta samu nasarar damke manyan barayin a cikin garin Birnin-Kebbi bisa ga bayanan sirri da a ke bayar wa ga jami’an nasa.

Ya kuma ce “muna kan binciken masu laifin, kuma da zarar an kammala zamu gabatar da su gaban kotu domin fuskantar hukunci”.

Wadanda ake zargi su ne Ibrahim Abubakar daga Jihar Sakkwato  da kuma Ibrahim Baga daga Unguwar Rafin Atiku da ke cikin garin Birnin-Kebbi. Daga nan kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da ba su goyon baya ta hanyar ba da bayanan sirri domin tabbatar da cewa sun dakile duk wata kafa da ake aikata laifuka a duk fadin jihar.