barayin shanu 15 sun tuba a Neja
barayin shanu 15 daga sassan Jihar Neja sun tuba a fadar Mai martaba Sarkin Lapai Injiniya Umar Bago Tafida da ke garin Lapai a jihar.Wata majiya wadda ta samu hira da wasu daga cikin tubabbun barayin shanun ta shaida wa wakilinmu cewa sun yi matukar nadamar ta’asar da suka dade suna aikatawa, inda suka ce […]
barayin shanu 15 daga sassan Jihar Neja sun tuba a fadar Mai martaba Sarkin Lapai Injiniya Umar Bago Tafida da ke garin Lapai a jihar.
Wata majiya wadda ta samu hira da wasu daga cikin tubabbun barayin shanun ta shaida wa wakilinmu cewa sun yi matukar nadamar ta’asar da suka dade suna aikatawa, inda suka ce a lokuta da dama har rugar Fulani suke zuwa su sace musu shanu.
Majiyar ta ce dalilin tubarsu ba ya rasa nasaba da yadda Alhaji Abubakar Salihu, Shugaban Matasan kungiyar Miyetti-Allah Kautal-Hore reshen Jihar Neja ya daura damarar ganin bayan barayin dabbobi da kuma masu garkuwa da mutane suna karbar kudin fansa.
Da yake jawabi a wurin taron, Alhaji Abubakar Salihu ya ce daga lokacin da ya daura damarar yaki da barayin shanu da masu garkuwa da jama’a ya kama akalla mutum 100 wadanda ya mika wa ’yan sanda domin hukuma ta dauki matakin da ya dace a kansu.
Shugaban Matasan ya ce, suna aikin ne kafada-da-kafada da wasu matasa daga ciki da wajen kungiyarsu.
Ya yaba kan hadin kan da jami’an tsaro ke ba su a wannan aiki da suka musamman shugaban ’yan sandan yankin.
Mataimakin Shugaban kungiyar Miyetti-Allah ta kasa shiyyar Arewa ta Tsakiya Alhaji Yusuf Hussaini Bosso ya nuna farin cikinsa da abin tarihin da ya faru a fadar Sarkin Lapai tare da yaba kokarin da masu yaki da barayin suke yi.
Mai martaba Sarkin Lapai Alhaji Umar Bago Tafida, ya roki Allah Ya ci gaba da taimaka wa jagoran masu yaki da barayin shanun kan matakin da ya dauka na tabbatar da jama’ar masarautar na ci gaba da walwala cikin kwanciyar hankali.
Alhaji Umaru Bago ya ce, “Mu a wannan masarauta muna alfahari da ayyukan alherin da kake yi. Akwai wata hanyar da barayi suka addabi jama’armu suka hana su sakat, kusan kullum sai an yi wa mutane fashin dukiyarsu, amma yanzu al’amarin ya fara zama tarihi. Mun ji dadin haka ka nuna mana kai dan kirki da al’umma ke bukatar irinsu.”