Barayin shanu: An dakatar da wasu hakiman Zamfara daga aiki

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta dakatar da wasu hakimai biyu daga mukamansu tare da tube rawanin wasu biyu bisa zarginsu da alaka da ‘yan fashin shanu da masu garkuwa da mutane. Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar, Alhaji Bello Dankande, ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai An tube rawanin hakimin Ruwan […]

Barayin shanu: An dakatar da wasu hakiman Zamfara daga aiki

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta dakatar da wasu hakimai biyu daga mukamansu tare da tube rawanin wasu biyu bisa zarginsu da alaka da ‘yan fashin shanu da masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar, Alhaji Bello Dankande, ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai

An tube rawanin hakimin Ruwan Gora Alhaji Ishaq Sadiq a  Karamar hukumar Bukkuyum da Hakimin Gundumar Gwalli Alhaji Musa Gwalli a Karamar Hukumar Gummi, yayin da aka dakatar Hakiman Gyadu da Tungar Dutse.