barayin shanu na cin karensu babu babbaka a Zamfara

Makiyaya a wasu kauyukan Jihar Zamfara sun shiga mawuyacin hali sakamakon addabarsu da barayin shanu suka yi a ’yan kwanakin nan. A ranar Asabar da ta gabata mazauna Kwanar Gambo kusa da Mayanci da ke karamar Hukumar Maru a jihar sun kwana cikin tashin hankali sakamakon hari da barayin shanu suka kai musu.daya daga cikin […]

barayin shanu na cin karensu babu babbaka a Zamfara
barayin shanu na cin karensu babu babbaka a Zamfara

Makiyaya a wasu kauyukan Jihar Zamfara sun shiga mawuyacin hali sakamakon addabarsu da barayin shanu suka yi a ’yan kwanakin nan.
A ranar Asabar da ta gabata mazauna Kwanar Gambo kusa da Mayanci da ke karamar Hukumar Maru a jihar sun kwana cikin tashin hankali sakamakon hari da barayin shanu suka kai musu.
daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa da misalin karfe 11:00 na dare barayin suka shigo musu, suka tara kowa da kowa a tsakar gida, suka karbe musu kudi da wayoyi sai dai ba su kashe kowa ba.
Sarkin Fulanin Mayanci Alhaji Dangana ya ce cikin dare barayin suka zo kuma sun kore masa shanunsa sama da 50 da na makwabta. Ya ce kafin zuwan maharan sun aiko da takarda cewa za su zo, su kuma sun sanar da jami’an tsaro amma babu wani taimako da aka samu daga gare su.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa kafin harin kauyukan da ke kewayen garin Mayanci sun tare a garin da dabbobinsu suna kwana a kasuwa da safe su tafi kiwo.
Makiyayan sun koka kan yadda sace-sace da kashe-kashen Fulani suka dawo a jihar, duk da ikirarin da gwamnonin shiyyar ke yi cewa barayin shanun sun kaurace wa jihohinsu.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Zamfara, DSP Sanusi Amiru ya ce ba su samu labarin harin ba amma za su gudanar da bincike a kai.