barayin shanu sun addabi gidajen gona a kewayen Abuja
Yankunan Ijah- Gwari da Ijah- Koro da ke karamar hukumar Tafa a Jihar Neja da suka kasance matattarar gidajen gona da mafi yawansu na masu hanu da shuni ne da ke Abuja a baya-bayan nan na fuskantar matsalar ta’addancin masu satar shanu. Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa daga ranar Talata 3 zuwa […]
Yankunan Ijah- Gwari da Ijah- Koro da ke karamar hukumar Tafa a Jihar Neja da suka kasance matattarar gidajen gona da mafi yawansu na masu hanu da shuni ne da ke Abuja a baya-bayan nan na fuskantar matsalar ta’addancin masu satar shanu.
Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa daga ranar Talata 3 zuwa Asabar 21 ga Yuni, barayin shanun sun auka wa gidajen gona hudu a yankin tare da kora shanunsu, baya ga rugagen makiyaya sama da biyar da a baya suka yi awon gaba da shanunsu.
Wani wanda matsalar ta rutsa da shi a ranar Asabar da ta gabata a wata ruga a yankin Ijan-Gwari, Malam Ahmadu Bawa ya bayyana wa wakilinmu cewa a lokacin da barayin shanun suka aukawa musu da misalin karfe 1:00 na dare sun bukaci ya sako musu shanunsa, daga bisani suka yi masa duka tare da sassara shi da makami.
Malam Ahmadu ya ce bayan barayin sun wuce ya yi yunkurin zuwa ga karamin asibitin yanikin, amma sai ya fadi a kasasakamakon zubar jini.
Hakimin Ijan Gwari, Malam Muhammad Sulaiman Sauki, wanda barayin suka shiga gidan gonarsa a ranar Talatar makon jiya suka saci shanu 31 da tumaki 15, ya nuna girgizarsa kan matsalar sace-sacen shanu a yankinsa.
Hakimin ya ce a lokacin da barayin suka shigo gonar, sun raunata ma’aikatansa saboda yunkurin da suka don fuskantarsu.
Ya ce ’yan sanda da ’yan banga sun yi yunkurin cim masu da aka sanar da su bayan awa daya da aukuwar lamarin, sai dai ya ce dabarar da barayin ta rarraba kansu da harbe-harbe daga wadanda ba sa tare da dabbobin, ya sa ba a gano inda suka yi ba. Ya ce da gari yawaye ne aka gano sun bi kurmin Gurara ne, lura da sawun dabbobin.
An yi wa wani gidan gona satar shanu 76 a ranar Asabar da ta gabata a Ijan-Koro da ke kusa da Bwari a yankin Birnin Tarayya, lokacin da barayin suka auka masa da karfe 12:30 na dare, kamar yadda daya daga cikin masu kula da wurin Sulaiman Idris ya shaida wa wakilinmu.
Ya ce bayan barayin sun balle dakin mahaifinsa wanda shi ne babban jami’in gonar da dakin da yake ciki da kanensa da wani daki da ma’aikatan gonar uku ke kwana, suka tara su wuri guda suka rika yi musu barazana iri-iri daga bisani suka sace da shanu 76.
A yayin farmakin, barayin ba sa raga wa tsofaffi ko mata, kamar yadda wani dattijo da ya ce shekarunsa sun haura 100, Alhaji Lautai Madugu da ke wata ruga a Ijan-Gwari ya bayyana.
Ya ce barayin sun bukaci ya nuna musu shanunsa, bayan ya ce ba sa kusa, sun yi ta dukansa kafin su wuce wurin ’ya’yansa inda suka walakanta matansu ciki har da mai ciki.
Wata mace a gidan gonar da ke kusa da garin Kuduru a Bwari, cewa ta yi a lokacin da barayin ke kokarin barin gidan gonarsu da shanun da suka sace, sun yi yunkurin tafiya da wata matar aure ’yar uwar mijinta. A cewarta bayan ta shaida musu cewa ba ta jima da haihuwa ba, barayin sun hakura ba su tafi da ita ba.
Baya ga dajin Gurara da ke Jihar Neja da ake zargi maboyar barayin shanu, akwai na Kawu a yankin Bwari, wanda aka ce ba masu bin shanunsu da aka sace ko jami’an tsaro ba su iya shiga cikinsa.
A zantawarsa da wakilinmu wani jagoran ’yan banga a garin Sabon Wuse, hedikwatar karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja, ya ce suna kokarin yaki da matsalar satar shanu a yankin, sai dai ya koka da matsalar karancin kayan aiki da tallafi daga bangaren gwamnati.