barayin shanu sun halaka makiyaya 164 a Taraba
Shugaban kungiyar Miyyeti Allah ta kasa reshen Jihar Taraba, Alhaji Mafindi danburam ya bayyana cewa barayin shanu sun kashe makiyaya 164 kuma suka sace shanu 17,000 a tsakanin 2013 zuwa bana a jihar. Ya yi korafin cewa, duk da irin wannan ta’asa da barayin shanu ke tabkawa a jihar, har zuwa yanzu ba wani da […]
Shugaban kungiyar Miyyeti Allah ta kasa reshen Jihar Taraba, Alhaji Mafindi danburam ya bayyana cewa barayin shanu sun kashe makiyaya 164 kuma suka sace shanu 17,000 a tsakanin 2013 zuwa bana a jihar.
Ya yi korafin cewa, duk da irin wannan ta’asa da barayin shanu ke tabkawa a jihar, har zuwa yanzu ba wani da jama’an tsaro suka kama. Ya ce shanu 700 kacal daga cikin shanun da aka sace aka samu nasarar kwatowa daga hannun barayin.
Ya ce kungiyarsu ta rubuta wasikun koke ga jami’an tsaro kan wannan lamari amma har yanzu an kasa shawo kan matsalar. Ya zargi wasu kabilu abokan zamansu da laifin satar mafi yawa daga cikin shanun nasu a Jihar Taraba.
Shugaban ya bayyana cewa shanu 400 ne sojoji daga Jihar Benuwai suka kwato daga hannun wani kasurgumin mai aikata laifi mai suna Gana, wanda ya ce ya tuba da aikata laifi har ma ya mika makamai masu yawan gaske ga jami’an tsaro.
Ya kara da cewa matsalar satar shanu ta zama babban lamari, wanda ke barazana ga tsaro a kasa, musamman a yakunan Arewa. Ya nemi gwamnati da ta dauki mataki cikin gaggawa, musamman a kananan hukumomin Donga da Bali da Wukari da Ibbi da Gassol da Takum da ke jihar Taraba, inda nan ne matsalar ta yi kamari.