Barayin shanu sun kashe jami’an tsaron CJTF 12 a Zamfara
Wasu da ake zargin barayin shanu ne dauke da makamai sun kashe jami’an tsaron farin kaya na CJTF 12 a Karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Jami’an tsaron wanda mafi yawancinsu ‘yan unguwar Kware da Kurya ne, lamarin ya faru lokacin da suke dawo wa daga wani taro da suka yi a garin Shinkafi, barayin […]
Wasu da ake zargin barayin shanu ne dauke da makamai sun kashe jami’an tsaron farin kaya na CJTF 12 a Karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Jami’an tsaron wanda mafi yawancinsu ‘yan unguwar Kware da Kurya ne, lamarin ya faru lokacin da suke dawo wa daga wani taro da suka yi a garin Shinkafi, barayin suka tare su suka fara bude masu wuta.
Wani mazaunin garin ya bayyana wa majiyarmu cewa, barayin sun yi wa jami’an tsaron kwantar bauna ne inda suka kai masu hari tare da kona buburansu a daji.