barayin shanu sun koma yin garkuwa da mata – FULDA
kungiyar Fulani da Makiyaya ta Jihar Kano (FULDA) ta koka kan yadda masu satar shanu suka canja salo zuwa garkuwa da mata suna neman iyalansu su biya kudin fansa.Shugaban kungiyar FULDA, Alhaji Usman Ahmad ya shaida wa Aminiya cewa sun fara sakin jiki suna harkokinsu, musamman da suka ga barayin shanun sun daina abin da […]
kungiyar Fulani da Makiyaya ta Jihar Kano (FULDA) ta koka kan yadda masu satar shanu suka canja salo zuwa garkuwa da mata suna neman iyalansu su biya kudin fansa.
Shugaban kungiyar FULDA, Alhaji Usman Ahmad ya shaida wa Aminiya cewa sun fara sakin jiki suna harkokinsu, musamman da suka ga barayin shanun sun daina abin da suke yi, sai kuma kwatsam suka bude wani sabon shafin na tsoratar da mutane.
kungiyar ta FULDA ta ce zuwa yanzu mata tara ne masu gakuwa da mutanen suka kama a kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada ciki har da matar mahaifin dan Majalisa mai wakiltar Doguwa a Alhaji Salisu Ibrahim Riruwai.
FULDA ta nemi gwamnati ta kawo musu dauki ta hanyar samar musu cikakken tsaro a garuruwan Fulanin musaman wadanda ke makwabtaka da dajin Falgore.
A tattaunawar Aminiya da dan majalisa Salisu Riruwai ya ce a safiyar ranar Alhamis ce masu garkuwa da mutanen suka je gidansu a garin Riruwai da ke karamar Hukumar Tudun Wada inda suka yi awon gaba da matar mahifinsa. “Kimanin ’yan bindiga 20 da suke dauke da miyagun makamai suka yi wa gidanmu tsinke inda suka tafi da matar mahaifina. Sun shirya dabara ce suka yi kururuwar neman taimako a kan cewa maciji ya sari wani mai suna Ibrahim. Lamarin da ya sa mutanen da ke gidan suka fito waje. daga nan suka kama dattijuwar suka sanya ta a mota suka tafi da ita,” inji shi.
Ya ce jim kadan da sace ta sai mutanen suka kira shi a waya suna neman ya biya Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansarta.
’Yan bindigar sun kuma sace wata mace mahaifiyar wani fitaccen mai maganin gargajiya da ake kira da Maitalan Serah.
Kwamishina ‘Yan sandan Jihar Kano Alhaji Muhamamd Musa Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce zuwa yanzu sun kama mutum hudu da akez argi da hannu cikin sace matan. Ya ce tuni jami’ansu na bangren yaki da garkuwa da mutane suka baza komarsu don gano inda barayin suka boye matan.