barayin shanu sun shiga hannu a Binin

Shugaban kungiyar ‘yan Banga reshen Jihar Edo, Alhaji Shuaibu Mohammed KT ya bayyana nasarar da kungiyarsu ta yi cikin wannan makon ta fasa gungun barayin shanu da suka addabi jama’a a dajin kauyen Aruakosa, mai tazarar kilo mita 17 daga garin Benin ta Jihar Edo.Ya ce a wannan fafatawar da suka yi da barayin sun […]

barayin shanu sun shiga hannu a Binin
barayin shanu sun shiga hannu a Binin

Shugaban kungiyar ‘yan Banga reshen Jihar Edo, Alhaji Shuaibu Mohammed KT ya bayyana nasarar da kungiyarsu ta yi cikin wannan makon ta fasa gungun barayin shanu da suka addabi jama’a a dajin kauyen Aruakosa, mai tazarar kilo mita 17 daga garin Benin ta Jihar Edo.
Ya ce a wannan fafatawar da suka yi da barayin sun samu nasarar cafke biyar daga cikinsu, inda sauran suka arce.
Shugaban kungiyar ’yan Bangar, Alhaji Shuaibu Mohammed KT ya shaida wa Aminiya hakan ne a ofishinsa da ke Eyaen a garin Benin.  Alhaji Mohammed KT, ya ce: ”Wadannan barayin labarinsu ya zo mana ne ta hanyar samun bayanan sirri daga wasu mutane a kauyen Aruokosa, wadanda suka sanar da mu mafakar barayin.
“Da isar mu kauyen muka shiga dajin wurin da  suka yi mana kwatance,  inda muka yi sa’ar tarar da wadannan miyagun a zaune, suna masha’arsu. Da ganinmu sai suka tasar mana haikan da rashin hankali. A nan muka yi dauki ba dadi da su, har muka samu muka kame mutum biyar daga cikinsu,  sauran kuwa suka baje mana kuramen itatuwa, inda a yanzu muke nemansu ruwa a jallo,”  inji shi.
Ya kara da cewa, wadannan barayin dubunsu ta cika ne a yayin da suka shiga wannan kauyen da tsakar dare, suka kwanto wani Bijimi sa da mutanen kauyen suka sayo, domin gudanar da wani bikin al’adarsu, suka kai suka daure shi a boye, cikin wani surkukin itatuwa na dajin.
Miyagun da suka shiga hannu su ne: Hashimu Bello Malumfashi da Mohammed Bello Katsina da Sule Bello Dayi da Ishaku Ahmadu Naija da Mohammadu Sani kwara. Wadanda suka gudu su ma da yardar Allah za su shiga hannu ba da  dadewa ba, a cewarsa.
A karshe Alhaji Muhammed KT ya bukaci jama’a da su ba kungiyarsu ta ’yan banga hadin kai da goyon baya, tare da bayanan sirri  na gaskiya game da duk wani mutumin da ba su yarda da shi ba.