…barayin shanu sun shiga hannu a Edo
Wasu da ake zargin barayin shanu ne da suka addabi masu kiwon shanu na kasuwar Benin, masu suna Muhammdu Hala da abokin aikinsa wani mahauci mai suna Ali Muhammad sun fada hannun ’yan banga a Benin ta Jihar Edo bayan da asirin wadanda ake zargin ya tonu lokacin da Muhammad Hala ya saci shanu tara […]
Wasu da ake zargin barayin shanu ne da suka addabi masu kiwon shanu na kasuwar Benin, masu suna Muhammdu Hala da abokin aikinsa wani mahauci mai suna Ali Muhammad sun fada hannun ’yan banga a Benin ta Jihar Edo bayan da asirin wadanda ake zargin ya tonu lokacin da Muhammad Hala ya saci shanu tara na wasu fatake .
Majiyarmu ta ce wanda ake zargi na farko Muhammadu Hala ya je garken Alhaji Elbade Muhammadu cikin dare ne ya ware shanu tika-tika guda tara ya tafi da su wani kauye da ake kira Oluku da ke daura da babban titin Benin zuwa Legas ya sayar wa Ali Muhammed, sannan ya sake zuwa kauyen Ahor ya hadu da wani abokin aikinsa mai suna Garba suka kora bijimai uku a cikin garken wani falke, kuma wadannan bajimai uku ne suka tona musu asiri ’yan banga suka kama su.
Muhammadu Hala mai kimani shakara 30 kuma dan asalin Jihar Borno, a cewarsa ya kai shekara 10 da zuwa Jihar Edo. “Aikina kiwo da kura-kura, ba ni da wani aiki bayan wannan don haka abin da ake zargina da aikatawa tsautsayi ne domin ban taba yin sata ba tun da nake, don haka ina neman afuwa daga masu dukiyar,” inji shi.
Shi kuma mahaucin Ali Muhammed mai kimanin shekara 35 da dan aslin karamar Hukumar Binji a Jihar Sakkwato, ya tabbatar wa ’yan banga a ofishinsu cewa ya sayi shanu biyu da Hala ya kai masa talla a wurin sana’arsa a Oluku, “lallai makonni biyu da suka gabata Hala ya kai min wasu shanu guda biyu ya ce min na wasu marayu ne sun ce ya sayar musu suna da bukatar kudi ban san cewa na sata ba ne dalilin da ya sa na saye su ke nan,” inji Ali.
Shugaban ’yan bangar Alhaji Shu’aibu Muhammed KT ya shaida wa wakilin Aminiya cewa “Muna tsare da Muhammadu Hala da abokin aikinsa Ali Muhammed amma za mu mika su ga ’yan sanda kuma muna neman sauran barayin da suka hada da Garba Gainako da Kabiru Mahauci da sauransu.”
Ya yi kira ga masu shanu da sauran jama’a a Jihar Edo su ba kungiyarsu ta ’yan banga hadin kai da goyon baya ta hanyar bayar da bayanan sirri game da masu aikata miyagun ayyuka domin magance ayyukansu a sassan jihar.