barayin shanu sun shiga hannu a Jihar Filato

A ranar Alhamis din makon jiya ne dubun wadansu barayin shanu su biyar ta cika, inda rundunar tsaro ta musamman (STF) a Jihar Filato ta cafke su dauke da shanun sata 12. Rundunar ta kuma kama wadanda ake zargin masu sayen shanun satar ne su uku, inda a halin yanzu ta mika su ga ofishin […]

barayin shanu sun shiga hannu a Jihar Filato
barayin shanu sun shiga hannu a Jihar Filato

A ranar Alhamis din makon jiya ne dubun wadansu barayin shanu su biyar ta cika, inda rundunar tsaro ta musamman (STF) a Jihar Filato ta cafke su dauke da shanun sata 12.

Rundunar ta kuma kama wadanda ake zargin masu sayen shanun satar ne su uku, inda a halin yanzu ta mika su ga ofishin ’yan sandan karamar Hukumar Shendam.
Rundunar ta bayyana hudu daga cikin barayin shanun wadanda suka ce su mutanen karamar Hukumar Langtang ta Kudu ne sun bayyana sunayensu da Marafa Nanbel da Banfa Adamu da Amos Luka da kuma Jerry Usaini, inda na biyar din kuma ya ce shi dan karamar Hukumar Kanam ne, kuma sunansa Sule Isa.
Rundunar ta ce wadanda aka kama da zargin sayen shanun sata masu suna Muhammad Abdulwahab da Al’amin Abubakar da kuma Bukar Muhammad, sun ce su dillalai ne ba barayin shanu ba, sun kuma sayi wadannan shanun ne a cikin kasuwar Garkawa da ke karamar Hukumar Langtang ta Arewa.
A yanzu dai wadanda ake tuhumar suna ofishin ’yan sanda na karamar Hukumar Shendam ana ci gaba da bincike a kan al’amarinsu.
Rundunar ta kuma bayyana kwato shanu 52 na sata tare da mika su ga Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta karamar Hukumar Miknag Alhaji Adamu Abdullahi don mayar da su ga masu su.
Kwamandan Rundunar Manjo Janar Dabid Enetie wanda Kanar Adam Hassan ya wakilta a lokacin da yake mika shanun a Shendam ya yi alkawarin za su ci gaba da fadi-tashi don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
“Za mu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da gajiyawa ba, hakan ne ya sa bayan mun ji labarin bacewar wasu shanu muka baza komarmu, inda a karshe muka kama wadanda ake zargi da satarsu, kuma a yanzu suke hannun ’yan sanda ana bincike kan al’amarin,” inji shi.