barayin shanu sun shiga hannu a Katsina

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta gabatar wa manema labarai wasu mutane da take zargi da satar shanu da tumaki a ranar Alhamis din makon jiya a hedkwatarta da ke garin Katsina.  Mutum 15 ne suka shiga hannu kamar yadda Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan jihar Bala Zamasanci ya ce, “Jami’anmu sun kama mutane ne a […]

barayin shanu sun shiga hannu a Katsina
barayin shanu sun shiga hannu a Katsina

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta gabatar wa manema labarai wasu mutane da take zargi da satar shanu da tumaki a ranar Alhamis din makon jiya a hedkwatarta da ke garin Katsina. 

Mutum 15 ne suka shiga hannu kamar yadda Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan jihar Bala Zamasanci ya ce, “Jami’anmu sun kama mutane ne a yankin Funtuwa inda muka yi nasarar samun shanu 232 da tumaki 141 da kuma sababbin babura biyu.”
Mataimakin Kwamishinan ya ce, barayin shanun sun kai hari ne a kauyen Kwangwai da ke yankin Funtuwa a ranar 7/2/2015 da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka je gidan wani mutum mai suna Babangida Usman suka yi awon gaba da shanu 50 da tumaki 40, ya ce, matakin gaggawa da jami’in ’yan sanda na yankin Funtuwa ya dauka ya sa suka yi nasarar kama mutum biyar da ake zargi.
Ya ce, jami’an ’yan sandan da ke aiki a yankin Makera sun kama wasu mutum 10 a ranar 11/2/2015 da misalin karfe 3:30, a harin da suka kai ga wani gungun Fulani da ake zargin barayin shanu ne da aka gan su a Unguwar Salla da ke yankin Funtuwa.
Mataimakin Kwamishinan ya ce an kwato shanu 182 da tumaki 101 da sababbin babura 2 da wayoyin salula 5 da adduna 5, kuma wadanda ake tuhumar sun ce sun sato dabbobin ne daga Jihar Zamfara, kuma tuni har wasu sun fara zuwa don gano dabbobinsu da aka sace.
Ya ce, daga cikin mutanen da suka kama har da yara uku wadanda a cewarsa, barayin suna amfani da su ne a wajen kiwon shanun da suka sace bayan sun samu wuraren da suke boyewa suna kallon abubuwan da suke gudana.
“A yayin da suka ga ’yan sanda sun tunkaro wurin da yaran ke kiwon sai su gudu su bar yaran,” inji shi.
Maitaimakin Kwamishinan ya ce, a cikin watan Janairun bana sun kama mutum biyar da shanu 533 da tumaki 61 da suke zargi na sata ne. Kuma sun kama mutum 30 da ake zargi ’yan fashi da makami ne, bayan bincike an kai 22 kotu yayin da 8 ana ci gaba da bincike a kansu.
Bala Zamasanci ya ce, sun kama motoci uku da suka hada da Carina E mai lamba AE 65 KNK da Honda Cibic, mai lamba AA 560 FKY da kuma Cienna mai lamba ABJ 705 da babura tara da ake zargin na sata ne, kuma har yanzu ana cikin bincike a kai.
daya daga cikin wadanda aka sace wa shanu a dajin Runka (Dajin Rugu), Alhaji Ibrahim Kankiya ya ce “Wani lokaci da rana suka same ni a cikin daji ina kiwo, sai kawai suka ce in je in nemi wata sana’ar in yi, amma shanu sun kwace, bayan sun nuna mini bindiga. Na yi niyar in ba su hakuri su bar mini wani abu daga ciki amma ina ji ina gani suka kora shanuna 200 da tumaki.”
Alhaji Ibrahim ya ce, tumaki 11 ne kadai ya gane a lokacin da ya ji an ce, an kama wasu barayin shanu a ofishin ’yan sanda da ke Funtuwa, amma shanu bai ga ko daya ba.