barayin shanu sun shiga hannu a Yobe

Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ta kama wadansu mutum 33 bisa zargin su da satar shanu kuma sun kashe akalla hudu daga cikinsu, tare da amso shanu kimanin 118 da tumaki 38 a samamen da ta kai maboyarsusu tare da hadin gwiwa da ’yan banga. Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa da ke […]

barayin shanu sun shiga hannu a Yobe
barayin shanu sun shiga hannu a Yobe

Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ta kama wadansu mutum 33 bisa zargin su da satar shanu kuma sun kashe akalla hudu daga cikinsu, tare da amso shanu kimanin 118 da tumaki 38 a samamen da ta kai maboyarsusu tare da hadin gwiwa da ’yan banga.
Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa da ke Damaturu Kwamishinan ’Yan sanadn Jihar Mista Markus danladi ya ce jami’ansa da hadin gwiwar ’yan banga sun samu nasarar cafke barayin ne a kauyen Karlere da ke karamar Hukumar Fika bayan da sun fafata da su.
Kwamshinan ya ce, rundunar ta kuma gano wasu makamai da barayin ke mafani da su wajen aikata ta’asarsu da suka hada da bindiga kirar AK 47 da jigidar harsasai kimanin 53 da wata karamar bindiga kirar gida.
Ya ce, daga cikin mutum 40 da suka kama 33 suna zargin ’yan fashi da makami ne da ke addabar jama’a a kananan hukumomin Fika da Gulani da Tarmuwa. Saura kuma sun gaza gamsasshen bayani ne aka kama su a kasuwar Damaturu.
Mista Markus ya ce, har ila yau rundunar ta yi nasarar hallaka wasu ’yan fashi da makami 3 da suka addabi karamar Hukumar Fika. Kwamshinan ya roki jama’a su ci gaba da tona aasirin batagarin da ke tsakaninsu ta yadda hakan zai taimaka wajen kawar da su a tsakanin al’umma.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi