Barayin wayoyi ne ke lalata fitulun titunan Abuja – Hukumar AMCC
Malam Shu’aibu Umara shi ne sabon Ko’odinetan Hukumar Gudanar da Birnin Tarayya, Abuja (Abuja Metropolitan Management Council -AMMC), a tattanwarsu da Aminiya ya ce hukumar za ta kwace lasisin lambunan shakatawa da aka gano suna aikata masha’a da badala a Abuja. Kuma ya ce barayin wayoyin wutar lantarki ne suke sanya birnin a cikin duhu […]

Malam Shu’aibu Umara shi ne sabon Ko’odinetan Hukumar Gudanar da Birnin Tarayya, Abuja (Abuja Metropolitan Management Council -AMMC), a tattanwarsu da Aminiya ya ce hukumar za ta kwace lasisin lambunan shakatawa da aka gano suna aikata masha’a da badala a Abuja. Kuma ya ce barayin wayoyin wutar lantarki ne suke sanya birnin a cikin duhu ta hanyar sace wayoyin fitulun kan tituna a cikin dare:
Mene ne ayyukan wannan hukuma taka?
Wannan wuri da nake shugabanta wato Hukumar Gudanarwar da Birnin Abuja (Abuja Metropolitan Management Council -AMMA) an kafa ta ce domin sa ido da tabbatar da bin ka’ida a tsarin gine-gine na gwamnati da na jama’a a daukacin yankin Birnin Tarayya Abuja tare da daukar hukuncin ladabtarwa a wuraren da aka saba ka’ida. Kamar yadda aka sani filin da aka ba da izinin gina gida yana bambanta da na kasuwanci haka na masana’anta, kuma tsarinsu ba daya ba ne. A dalilin haka ana bukatar kafin a fara gina wuri ko sauya fasalinsa sai an samu amincewar wannan hukuma. Idan kuwa muka gano an samu akasin haka, to hukumarmu za ta dakatar da aikin, sannan idan ya saba da tsari a rusa bayan mun bi dukan ka’idojin da su ka kamata. A takaice hukumar ce ke kula da wuraren da Hukumar Raya Birnin Tarayya, Abuja (FCDA) ta gina da daukacin sauran gine-gne da ke birnin.
Kamar wadanne bangarori ne ke karkashn wannan hukuma ta AMMC?
Akwai bangaren kula da gine-gine wato Debelopment Control, akwai na gyaran wurare wato Facilities Maintenance Department, akwai na wuraren ajiye motoci da kuma wuraren shakatawa kamar lambuna wato Park and Recreation, akwai na duba-gari wato Abuja Enbironmental Protection Board da bangaren kula da allunan sanarwa na kan hanya da bangaren kai-daukin gaggawa da sauransu. Wadannan su ne bangarori da muke aiki tare da ke karkashin wannan ma’aikatar.
A baya an rusa wasu gine-gine da suke wurare masu yanayin fadama a tsakanin unguwanni aka maida su wuraren hutawa na al’ummar yankunan, sai dai a yanzu wasu daga cikinsu sun zama cibiyoyin masha’a, me kuke yi a kansu?
Wannan gaskiya ne, mun samu wannan matsala kuma a dallin haka mun kafa kwamiti da zai gudananar da aikin tantance wuraren, inda za a bukaci takardun izinin gudanarwa daga wajen ma’abotansu tare da tantance ko sun bi ka’idar gudanar da su. Idan mutum ya ki kawowa ko ya kawo aka gane cewa ya saba ka’idar muna da ikon kwace wurin.
Akwai zargin cewa ana anfani da wasu wurare da ke matsayin cibiyoyin kula da marayu ana safarar yara kun samu wannan bayani?
Wadannan cibiyoyi ba sa karkashinmu, suna karkashin Sakatariyar Kula da Al’amuran Jama’a ta Abuja ce, wato Human Resource Secretariat. A can ne ya kamata a kai korafi idan ana da zargi irin haka, wanda in ya tabbata sai su dauki matakin soke lasisisinu.
Kusan dukan titunan birnin Abuja na da fitila sai dai kadan daga cikinsu ne suke aiki a baya-bayan nan, me ya faru?
Matsalar da ake samu a fitilun titunan Abuja yawanci suna faruwa ne dalilin ayyukan masu sace wayar wuta wadda ke faruwa cikin dare musamman a lokacin da aka dauke wutan lantarki. Masu aikata ta’asar sun san inda wayoyin suke kwance a cikin bututu, saboda haka da sun ga an dauke wuta sai su datse waya kuma ko da mota ce ta jami’an tsaro ta zo wucewa a lokacin sai su kwanta har sai motar ta wuce su ci gaba da aikinsu. Sai dai muna daukar sababbin matakai da muke fatan za su magance matsalar.
Ministan Abuja ya yi yunkurin karasa aikin Babbar Kasuwar Abuja da ke Deidei da ake sa ran za ta rage cinkoso a cikin birnin, sai dai shiru ake ji, me ke faruwa?
Ana nan ana shirin aikin. Ba a jima ba na ziyarci kasuwar don tantance abubuwan da take bukata kafin ta fara ci. Kuma ina nan ina shirya bayanin abubuwa da kasuwar ke bukata wadanda suka hada da gina babbar hanya da za ta sada kasuwar da wasu wurare masu muhimmanci don mikawa ga Mai girma Minista nan ba da jimawa ba.