barayin zaune (2)
Lallai wadanda muka lissafa a wancan karon ba su ne kadai barayin zaunen da muke da su ba a cikin kasar nan, muna dai iya cewa su ne hamshakai, su ne, gandama-gandama, su ne kuma masu kawo illa ga kasa da sauran lamurran rayuwa. Daga Kansila zuwa Shugaban kasa da sauran manya kuma hamshakan masu […]
Lallai wadanda muka lissafa a wancan karon ba su ne kadai barayin zaunen da muke da su ba a cikin kasar nan, muna dai iya cewa su ne hamshakai, su ne, gandama-gandama, su ne kuma masu kawo illa ga kasa da sauran lamurran rayuwa. Daga Kansila zuwa Shugaban kasa da sauran manya kuma hamshakan masu dukiya da ’yan kwangila da ’yan korensu, nan ne ake da dabar masu sunkurun ganin bayan talaka da neman sai sun ga bayan kasar da suke wa ‘hidima.’ Idan da abin a zauna a kididdige tarin dukiyar da wadannan gungun mutane suka sace, (kamar yadda gwamnatin Buhari ta fara yi yanzu) suka kimshe ne, suke wandaka da ita, za mu fahimci cewa ashe ba laifi ba ne idan sama da miliyan 100 na al’ummar kasar nan suka kasance cikin tasku da talauci da fatara da shiga cikin kowane irin halin ni’yasu na rayuwa. Ke nan ba abin mamaki ba ne da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya jaddada mana wadannan ’yan uwan Ali Baban wannan zamani. Amma ba su kadai ba ne, akwai wasu barayin can boye wadanda kila ma sun fi wadannan da Balarabe Musa ya zayyana barna da tayar da hankali. Su wane ne wadannan?
Mu koma ga jawabin da Balarabe Musa ya yi, ya ce ne matsalar kasar nan ta bARAYIN SHUGABANNI ce. Ke nan ba dole sai shugabannin siyasa ba, za a iya samun wasu gungun barayin daga cikin shugabannin addini da na tattalin arziki da saye da sayarwa da kasuwanci da na sauran al’umma da suka hada daga Sarakuna da Hakimai da Dagatai da Masu unguwannin.
Haka kuma bisa lissafin Balarabe Musa, duk da bai fito karara da alkalumman ba, yana iya hadawa da shugabanni a kasuwa da makarantu da cikin gidajenmu, wato tsakanin iyali. Ke nan muna iya cewa barayin suna da yawa! Ta yaya za mu gane irin wadannan shugabanni da irin tasu barnar da suke yi wa kasa da al’umma?
Mu soma da shugabannin addini, ba sai na yi ta mawakin nan Fela ba, da yake cewa ka taba ganin inda Fasto ko Fada ko Liman ko Ladan ko wani rikakken malamin addini da ya kasance talaka? kila ka ce ai naka malamin ga shi nan kwance cikin talauci da rashi, kila domin shi ba shugaban ba ne na gaskiya, da kila tuni ya yi hannun riga da wahala da tashin-tashina.
Amma nawa daga cikin shugabannin addinin da muke da su a cikin kasar nan suka kasance talakawa? Nawa suke yawo da jiragensu na kansu a sararin samaniya? Nawa ke cikin daular aljannar duniya; su ne da jifa-jifai da manya-manyan gidaje da zuwa yawon bude idanu a kasashen duniya, a lokacin da suka so, yadda suka so, alhali ko aikin kwarai ko wata sana’ar kirki ba su da ita? Nawa daga cikin shugabannin addinan da muke da su za mu iya kira mutanen talakawa ko masu son talakawa ko da ba mu kira su barayi ba kai-tsaye? Nawa? A fa lura, shi wannan shugaban addinin da ke faman bayyana mana inda wuta ko Aljanna suke da sakamakon wadanda suka saba wa Maiduka, wasu ba su ma yarda akwai gobe kiyamar ba, balle wani abu wuta ko Aljannar. Idan ka yi maganar Aljanna, ga irin wadannan malamai, sai ka ji suna maganar Aso Rock ko fadojin gwamnonin jihohi ko ofisoshin ministoci ko kwamishinoni ko shagunan hamshakan ’yan kwangila ko kuma unguwannin Asokoro ko bictoria Island ko makamantansu. Nan ne aljannarsu! Idan kana ji suna maganar wuta, to rashin samun kwangila ce, ita ce wuta a gare su. Wata wutar ita ce rashin wata hanyar da za su diba daga tarin dukiyar al’umma.
Duk lokacin da hakarsu ba ta kai ga ruwa ba lokacin ne zafi ke damunsu, lokacin ne suke tuna akwai wata aba wai ita wuta, ba wai don sun amince da akwai ta can a Lahira ba!
Shin ba mu san da irin wadannan shugabannin addinin ba ne? Shin su kuma me ya raba su da sauran barayin da Balarabe Musa ya zayyana mana? Mu dinga yi wa kanmu kiyamullaili fa! Mu lura da irin badakalar da ke faruwa yanzu ta bankado barayin zaune da wannan gwamnati ke yi, abubuwa za su kara bayyana. Amma irin wadannan barayin su ke nan muke da su?
Ba wadannan kadai ba ne, shin ina barayin da suke zaune cikin kasuwanci da tattalin arzikin kasar nan, ba su da daki ko falo ko wurin shakatawa sai dukiyar kasa da ta al’umma? Wane ne zai ce da ni yawancin shugabannin da muke da su, masu kamfanoni da masana’antu, bilahaddin, su kuma masu ceto ne ba cutarwa ba? Don Allah wane irin kasuwanci ko sana’a wadannan manya, kuma hamshakan masu ‘kudi’ suke yi da suke tarawa da samun wannan kazamar riba? Wasu daga cikinsu, sun ma fi gwamnatin kasar tarin dukiya, kuma wai sana’a ce suke yi? Sai mu tambayi kanmu, wace irin sana’a ce wannan da ke sa yara ’yan shekara 30 zuwa 35 ke samun tarin dukiyar da ta fi ta wata gwamnatin jiha? Wace sana’a ce wannan? Wasu za su ce ai kwangila suke yi, amma mu tambayi kanmu shin kwangila aikin yi ne ko wata sana’a ta a zo a gani? Shin me ya bambanta dan kwangila irin wannan zamani namu da barawo? Me ya bambanta satar da shugabanninmu na siyasa ke yi da irin wadda ’yan kwangila da hadin bakin shugabanninmu ke yi, cewa nake, Ali ne ya ga Ali! Ke nan shugabannin sana’o’i da kwangiloli su ma barayin ne!
Haka batun yake a fannin harkar ilimi da kiwon lafiya da sauran al’amuran zamantakewar al’umma. Hedimasta a Firamare barawo ne, Firinsifal a Sakandare, ba shi dama, satar zai yi, balle irin su Rekto da Furobos da Shugabannin jami’i’o, duk dai jama’ar ce ta Gambu! Ke nan duk inda ka samu shugaba, komai kankantar wurin da yake shugabanci sai ka ga dan hali ya bayyana. Shi ya sa a harkar asibiti ba fus. Harkar gina hanyoyi da sa kwalta da gina azuzuwa ba shugabannin kwarai, sai macuta!
Ke nan harkar sata a Najeriya ta riga ta zama ruwan dare, domin kuwa ba ta bar kowane shugaba da tsarin shugabancin da yake yi ba. Ina shugabannin kwadago? Ina shugabannin ’Yan Yuniyon da masu tura baro da masu faskare da ’yan-ga-ruwa da shugabannin mata masu adashi da kungiyar malamai tun daga Firamare zuwa Sakandare da Jami’o’i? Ina maigida da gidansa? Ina matarsa da ’ya’ya? Ina mai sayar da man gyada da tumatir a kasuwar kauye? Su wadannan ba barayi ba ne?
Za mu ci gaba